Xabi Alonso ya yanke shawarar ci gaba da zama a matsayin mai horas da ’yan wasan ƙungiyar Bayer Leverkusen da ke buga Gasar Bundesliga a Jamus.
Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da farin jinin tsohon ɗan wasan na ƙungiyar Real Madrid ke ƙaruwa bayan manya ƙungiyoyi sun shiga zawarcinsa.
Sai dai sanarwar da ya yi ta yanke shawarar ci gaba da zama a Bayer Leverkusen ta ankarar da ƙungiyoyin da ke kan gaba wajen zawarcinsa — Liverpool da Bayern Munich — da su gwada sa’arsu a kan wani kocin daban.
Kocin wanda ɗan asalin Sifaniya ne, ya samu farin jini musamman wajen manyan kulob ɗin biyu, sakamakon cewa masu horar da su za su yi murabus daga jagorancin su a ƙarshen kakar bana.
Tuni Liverpool ta sanar da tafiyar kocinta na yanzu, Jorgen Klopp, haka ita ma Bayern Munich za ta rabu da kocinta, Thomas Tuchel da zarar an kammala kakar ta bana.
Leverkusen dai ƙarƙashin Xabi Alonso tana dab da ɗaukar kofin Bundesliga a karon farko a tarihin ƙungiyar, inda a wannan shekarar sun yi zarra wajen rashin shan kaye a wasannin da suka buga a duka gasannin da suke ciki.
Alonso ya sanar wa taron manema labarai cewa ba zai amshi tayin horar da Bayern Munich ba, duk da sun rigaya ambata shi a matsayin wanda suke fatan miƙa wa ragamar ƙungiyar.
Tun ranar Alhamis ne alamu suka nuna cewa Liverpool ta haƙura da neman Alonso, wanda tsohon ɗan wasanta ne a zamanin da yake buga ƙwallo, domin ya maye gurbin kocinta Jurgen Klopp.
Da yake magana da ’yan jarida, Alonso ya ce, “Mun ji raɗe-raɗi daban-daban game da makomata. Ina so na yi amfani da hutun nan don yin tunani da yanke hukunci. A makon baya na sanar da kulob ɗina cewa zan ci gaba da zama koci.
“Aikina a nan bai ƙare ba. Ina ganin nan ne ya dace da ni na zauna, kuma na inganta aikina na horar da ’yan ƙwallo.”
Alonso yana da shekaru 42 a duniya, kuma yana da burin cin kofuna uku a bana, inda Bayer Leverkusen take da fifikon maki 10 a teburin Bundesliga, kuma ta kai matakin ƙarshe na gasannin DFB-Pokal da kuma Europa League.
Tunda hankalin Leverkusen ya kwanta yanzu, ƙungiyar tana fatan ƙarasa aikinta inda take fatan nasara a wasanta da Hoffenheim ranar Asabar, kafin ta koma kan wasan dab da na ƙarshe a kofin Dusseldorf a tsakiyar mako.