✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Zargin N96bn: Wike ya sake maka Amaechi a kotu 

Gwamnatin na zargin Amaechi da yin sama da fadi sa biliyan 96 lokacin da yake gwamnan jihar.

Gwamnatin Ribas ta shigar da sabuwar kara kan tsohon gwamnan jihar kuma tsohon Ministan Sufuri, Rotimi Amaechi, kan zargin yin sama da fadi da Naira biliyan 96.

An maka Amaechi tare da Tonye Cole, dan takarar gwamna na Jam’iyyar APC a jihar bisa zargin sayar da kadarorin jihar.

Zacchaeus Adangor, babban lauyan Gwamnatin Jihar Ribas, ya tabbatar da shigar da karar.

Nyesom Wike, gwamnan Ribas, ya kafa wani kwamitin mutum bakwai don bincikar Amaechi kan zargin cirar Naira biliyan 96 daga asusun gwamnatin jihar a lokacin da yake gwamna.

Kwamitin ya kuma binciki batutuwan da suka shafi sayar da kadarorin da tsohon gwamnan ya yi.

Kwamitin ya gabatar da rahotonsa a 2015 kan binciken, amma Amaechi ya musanta aikata laifin da ake tuhumar sa.

A ranar 27 ga Mayu, 2022, wata babbar kotu ta yi watsi da bukatar Amaechi na hana kwamitin gudanar da bincike a kansa.

Sakamakon haka ne, Wike, ya umarci babban lauyan jihar da ya gurfanar da tsohon gwamnan tare da  Tonye Cole da wasu mutum biyar da ake zargin na da hannu a badakalar.

Wike ya kuma umarci a shigar kan kamfanin Sahara Energy, wanda ake zargin an yi amfani da shi wajen satar kudaden.

A watan Oktoban 2022, Okogbule Gbasam, Alkalin Babbar Kotun Jihar Ribas, ya dakatar da tuhumar da ake yi wa kamfanin.

Wannan dai ba shi ne karon farko da gwamnati mai ci ke bincike kan gwamnatocin da suka shude ba, kan zargin cire makudan kudade ba bisa ka’ida ba.

A wasu lokuta ana zargin siyasa a cikin lamarin, da nufin daukar fansa musamman idan ya kasance akwai adawa a tsakani.