Makon da ya shige; mun soma koyarwa kan almajiranci irin na Kirista; dalilin kuwa shi ne masu bi da yawa sun yi watsi da wannan umarnin da Yesu Kiristi ya bar mana. Yawancin lokaci wasu da dama ba su san irin abin da suke hasaransu ba, domin rashin kiyaye wannan umarni, shi ya sa ina so ne mu gane ko mene ne wannan almajiranci, mu kuma iya sa kanmu ciki sosai. A yau za mu ci gaba da ba da ma’anar almajiranci.
Almajiranci dai za a iya kwatantawa da irin zumuncin da ke tsakanin maigida da mai koyon aiki ko malami da dalibi; irin wannan zumunci kuwa yana da shiryayyen tsari da hanyoyin gudanarwa. Abu na farko da ya kamata mu yi la’akari da shi kuwa shi ne: muna magana ne game da zumuncin da ke akwai tsakanin Kirista da shi Ubangiji Yesu Almasihu. Shirin koyo ne da mutum da kansa zai kawo kansa karkashin Ubangiji Yesu da burin zama kamarsa. A cikin Littafin Luka 6:40, maganar Allah na koya mana cewa: “Almajiri ba bisa kan malaminsa yake ba; amma kowa sa’anda ya kamalta za shi zama kamar malaminsa.” Wannan abin lura ne kwarai da gaske ga duk wanda yana so ya bi Yesu Kiristi. daya daga cikin hanyoyin da Ubangiji Allah Yakan mora shi ne, Yesu Kiristi yakan nada wadansu daga cikin almajiransa domin su almajirantar masa da sauran. Shi ya sa bai kamata mu yi wasa da wannan babban umarni ba ko kadan. Yesu Kiristi da kansa ya ce mana cikin magarsa: “Ku dauki wa kanku karkiyata, ku koya daga wurina, gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai sauki ce, kayana kuma mara nauyi.” (Matta 11: 29 -30).
Yesu ya ba da wannan umarni ga dukan mabiyansa, wato waddnda suka rigaya suka ba da gaskiya da shirin ceto wanda Allah da kanSa Ya shirya cikin matuwar Yesu Kiristi da kuma tashinsa daga matattu. Yesu Kiristi bayan da ya tashi daga kabari, sai ya ce wa sauran almajiransa “Ku tafi fa, ku almajirantar da dukan al’ummai, kuna yi masu baptisma zuwa cikin sunan Uba da na da da na Ruhu Mai tsarki. Kuna koya musu su kiyaye dukan iyakar abin da na umurce ku; ga shi kuwa ina tare da ku har matukar zamani. (Matta 28:19 – 20). Idan har mutum yana so ya bi sawayen Yesu Kiristi a wannan duniya dole ne ya yi biyayya ga wannan umarni.
Almajiranci yana da wurin farawa, ko mu ce mashiga ko mafari, wannan mafari ba ya faruwa cikin rashin sanin shi dalibin ko malamin; ana somawa da cikakken sani. Wannan mashiga kuwa ita ce sa’ar da dalibi yake mika wuyarsa ga karkiyar Ubangiji bisa ga yardar ransa domin koyo daga wurinsa. Har yanzu za mu sake karatu daga cikin Littafin Matta 11: 28 – 30 da take cewa “Ku zo gare ni, dukanku da kuke wahala, masu nauyin kaya kuma, ni kuwa in ba ku hutawa. Ku dauka wa kanku karkiyata ku koya daga wurina; gama ni mai tawali’u ne, mai kaskantar zuciya: za ku sami hutawa ga rayukanku. Gama karkiyata mai sauki ce, kayana kuma marar nauyi.”
Haka nan muka gani a cikin Littafin Sarakuna na Fari, sura goma sha tara: 1Sarakuna 19: 19 – 20; maganar Allah na cewa “Ya fa tashi a wurin, ya iske Elisha dan Shaphat yana noma da shanu bibbiyu har goma sha biyu a gabansa, yana kuwa tare da na goma sha biyu din; Iliya kuwa ya wuce har zuwa wajensa, ya jefa masa mayafinsa a jiki. Sai ya bar shanu, ya yi gudu ya bi Iliya, ya ce, ina rokonka ka bar ni in yi wa ubana da uwata sumba tukunna, kana in bi ka. Ya ce masa, Sai ka juya ka koma; gama me na yi maka?”
Wannan labarin Annabi Iliya ne da sabon almajirinsa Elisha. Akwai mafarin wannan almajiranci a tsakaninsu. Ba zai taba yiwuwaba ka zama almajirin wani malami ba tare da saninsa ba. Haka nan kai dalibin ko almajirin. Daga inda muka yi karatun nan, shi Annabi Iliya ya dauki Elisha cikin zaman almajiranci domin ya shirya shi da nufin cewa Allah zai yi amfani da shi nan gaba.
Almajiranci, hanyar kamantuwa ne da surarsa; wannan kuwa ba zai faru kawai domin mun sadu da shi sau daya ko biyu kawai ba. Ya kunshi matakan koyarwa, horarwa da za a bi a hankali har sai nufin Allah ya cika a cikin rayuwar mutum. Ba kawai shirye-shiryen wata bita ko wasu ayyuka ba ne, amma cudanya ne, hadin rai ne wanda ba a gani da ido, hanyar shigowar sabuwar rayuwa a maimakon tsohuwar. Wannan irin canji cikin yanayin rayuwa yana kama da karamin yaro da yake koyon yin tafiya – wato; akwai faduwa da kuma tashi idan an fadi: Wani lokaci ma kana iya yin kuka har da hawaye. Dalili kuwa shi ne, duk mutumen da ya saba da rayuwarsa ta aikata zunubi na shekaru da dama, ba zai taba iya yarda da sauki domin ya canju ba, kamantuwa da sabuwar siffar nan na iya kawo damuwa sosai ga wanda bai saba ba, amma a karshe abin alheri ne. Maganar Allah na cewa cikin Littafin Ayuba 5 : 17 -18 “Ga shi, mai farin ciki ne mutum wanda Allah ke tsawatar masa; kada fa ka raina horon mai iko duka. Gama yakan sa cuta, ya kuma samar da magani, Yakan sa rauni, hannuwansa kuma su bada lafiya.” Mutane sukan fi ganewa da tsohuwar hanyar rayuwarsu fiye da wata sabuwar hanya. Idan kuwa har mutum yana so ya ga canji cikin rayuwarsa, dole ne yana bukatar zumunci na kusa da kusa da Ubangiji da kuma iyayen goyo da Allah ke mora domin rainon almajirin.
A cikin Littafin Misalai 3 :12 maganar Allah tana cewa “Gama wanda Ubangiji yake kauna shi yake tsawata masa: Kamar yadda uba yakan yi wa dan da yake jin dadinsa.” Idan mun iya jure horon Ubangiji, a karshe babu shakka za mu yi rayuwar da za ta gamshe shi a koyaushe: gama wanda Ubangiji ke kauna, shi yake horo, Yana kuwa dukan kowane dan da yake kaba.
Almajiranci abu ne da dole ne mu kawo kanmu ciki idan har muna so mu cika nufin ubangiji Allah.
Mu ci gaba da yin addu’a domin kasarmu da kuma wannan lokaci na siyasa. Mu roki Ubangiji Allah Ya ba mu salama da zaman lafiya cikin kasarmu. Idan Allah Ya bar mu cikin masu rai; za mu ci gaba da nazarinmu. Ubangiji Allah Ya taimake mu duka, amin.
Almajiranci irin na Kirista (3)
Makon da ya shige; mun soma koyarwa kan almajiranci irin na Kirista; dalilin kuwa shi ne masu bi da yawa sun yi watsi da wannan…