Sarkin Lafiagi Alhaji Sa’adu Kawu Haliru ya koma ga mahallicinsa ranar Alhamis; ya rasu yana da shekara 86 a duniya.
Sarkin ya rasu ne da yammacin ranar Alhamis a wani asibiti da ba a bayyana sunansa ba a Abuja, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Wata majiya ta bayyana cewa za a dauki gawar Sarkin ranar Juma’a zuwa garin Lafiagi da ke Karamar Hukumar Edu a jihar Kwara.
Marigayin ya hau karagar mulki tun a shekarar 1975, sannan an yi bikin cikarsa shekara 45 yana sarauta a ranar 21 ga watan Oktoban 2020.
Da ya ke tabbatar da rasuwar Sarkin, daya daga cikin masu nadin sarki, Ndegin Lafiagi Alhaji Ahmed Kaiama, ya bayyana rasuwar a matsayin babban rashi ga al’ummar Nufawa baki daya.
Sakon ta’aziyya
Marigayin ne Shugaban Hukumar Rediyon Jihar Kwara na farko.
Gwamnan Jihar ta Kwara, Abdulrahman Abdulrazaq, ya aike da sakon ta’aziyyarsa ga daukacin al’ummar jihar kan rasuwar Sarkin.
Sakon ta’aziyyar, wanda jami’n hulda da ‘yan jarida na gwamnatin Jihar, Rafiu Ajakaye, ya fitar ya ce, “Ina yi wa daukacin al’ummar Kwara ta Arewa da ta Kudu da ta Tsakiya ta’aziyyar rasuwar Sarkin Lafiagi, Alhaji Sa’adu Kawu, OFR.
“Sarkin mutum ne mai kawaici, hazaka, son zaman lafiya da aiki don hadin kan al’ummarsa.
“Ina mika sakon ta’aziyyata ga Masarautar Lafiagi, iyalansa da ‘yan uwa da abokan arziki kan wannan babban rashi.
“Mutuwar Sarki tabbas babban rashi ne wanda ya kawo karshen shekara 45 da ya yi yana mulkin Lafiagi.
“Ina addu’ar Allah Ya yafe masa kurakuransa, Ya sa shi a Aljannar Firdausi”.