✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa Sarkin Kauru rasuwa

Sarki Ja’afaru Abubakar ya rasu yana da shekara 74 bayan fama da rashin lafiya

Sarkin Kauru a Jihar Kaduna, Alhaji Ja’afaru Abubakar, ya rasu bayan fama da rashin lafiya yana da shekara 74  a duniya.

Dan uwan mamacin kuma Jarman Kauru, Malam Sulaiman Lawal ya bayyana marigayi Sarkin Kauru Ja’afaru Abubakar da cewa mutum ne mai tsoron Allah da za a yi matukar kewar sa.

Ya ce babban burin mamacin, wanda ya bar mata hudu da ’ya’ya hudu shi ne ganin Masarautar Kauru ta samu ci gaba.

Sarakin Kauru Ja’afaru wanda ya hau karagar mulki a shekarar 1993, ya rasu ne a Asibitin Koyarwa na Barau Dikko da ke garin Kaduna a ranar Alhamis, sannan aka yi jana’izarsa a ranar Juma’a a garin Kauru.

A ranar Lahadi Mataimakiyar Gwamnan Jihar Kaduna, Dokta Hadiza Sabuwa Balarabe, ta jagoranci tawagar Gwamnatin Jihar zuwa Masarautar Kauru da ke Karamar Hukumar Kauru domin yin ta’aziyya.