✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Allah Ya yi wa kakar Abba Gida-gida rasuwa

Kakar dan takarar Gwamnan Kano a Jam'iyyar NNPP ta rasu tana da shekara 103

Hajiya Mowa Sufi Yakasai, kakar dan takarar Gwamnan Jihar Kano a Jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf, ta rasu.

Hajiya Mowa Yakasai ta rasu tana da shekara 103 bayan gajeriyar rashin lafiya.

Za a yi jana’izarta a fadar Sarkin Kano bayan Sallar Juma’a.

Ta rasu ta bar ’ya’ya da jikoki da dama daga cikinsu akwai dan takarar gwamnan Jihar Kano na jam’iyyar NNPP, Abba Kabir Yusuf da kuma likita a Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad, Dakta Atiku Musa.

Fitattun ’ya’yanta sun hada da tsohon Sakataren Ilimi na Kwalejin Addini da Shari’a ta Aminu Kano, Ibrahim Abubakar Aminu.