✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Allah Ya yi wa jarumin Kannywood Umar Malumfashi rasuwa

Marigayin ya rasu ne a Yammacin ranar Talata bayan sallar Magariba.

Allah Ya karbi rayuwar Umar Malumfashi wanda aka fi sani da Yakubu Kafi Gwamna a cikin shirin Kwana Casa’in mai dogon zango.

Marigayin ya rasu ne a wani asibiti da ke unguwar Hausawa bayan Masallacin Murtala da ke Kano a Yammacin ranar Talata bayan sallar Magariba.

Yakubu shi da Tijjani Faraga a lokacin yana jinya a Asibiti (Hoto: Tijjani Faraga)

Tijjani Faraga, daya daga cikin manyan jaruman Kannywood da ya ziyarci mamacin a lokacin yana jinya ne ya tabbatar wa da Aminiya hakan.

“Eh wallahi dazun nan ya rasu.

“Don ya kwanta jinya a asibiti kusan sau uku, kuma da yake cutar ba ta tashi ba ce ita ce ajalinsa.

“Allah Ya yi mishi rasuwa, zuwa gobe Laraba da safe za a yi jana’izarsa,” a cewar Tijjani.

Umar Malumfashi wanda ya shafe fiye da shekaru 30 ana damawa da shi a wasannin kwaikwayo, ya fi shahara da sunan Bankaura wanda ya samo asali tun a shekarun 1980 yayin wani shiri da gidan tsohon gidan talabijin na CTV yake haskawa.

Yana daya daga cikin jaruman wasan kwaikwayo da suka yi zamani da marigayi Kasimu Yero, Usman Pategi (Samanja) da Garba Ilu da sauransu.