Rahotanni da muka samu a yanzu sun nuna cewa Allah Ya yi wa Abdulwahab Awarwasa rasuwa a wannan Litinin din.
Sanarwar rasuwar jarumin na masana’anatar shirya fina-finai ta Kannywood ta bulla ne a dandalin sada zumunta na Facebook.
- Martinez Zogo: An tsinci gawar dan jaridar Kamaru da aka sace
- Kotu ta ba da umarnin gurfanar da Tukur Mamu
A sakon da mai shirya fina-finai Falalu A. Dorayi ya wallafa, ya ce “InnalilLahi wa inna ilaiHi raji’un. Allah ya jikan Abdulwahab.
“Allah Ya yu masa gafara Ya ba wa iyalansa, iyaye da ’yan uwa hakurin rashinsa.
“Idan mutuwar ta zo Allah Ka sa mu cika da imani. Amin.”
Hakazalika, masu ruwa da tsaki da masoya da dama sun yi ta wallafa hotunan Awarwasa tare da sakonnin Allah Ya jikan rai.
Marigayi Awarwasa na daya daga cikin taurarin da suka haska a cikin shirin fim din nan mai suna A Duniya.