Inna lillahi wa inna ilaihir raji’un! Rahoton da ke shigo mana yanzu na cewa, Allah ya yi wa tsohon shugaban Najeriya, Alhaji Shehu Shagari, rasuwa.
Gwamnan jihar Sakkwato, Aminu Waziri Tambuwal, ya tabbatar da wannan rahoton a shafinsa na Tiwita da yammacin yau Juma’a misalin karfe 7:30.
Marigayin ya rasu ne a babban asibitin Abuja. Ya rasu yana da shekaru 93.
Allah ya ji kanshi da rahama Amin.