Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ce Allah ne kadai Ya san jamiyyar da za ta karbi mulkin jihar daga hannun gwamnatinsa.
Ganduje ya yi wannan furuci ne kwana 24 kafin ya sauka daga mulki, a yayin kaddamar da wasu ayyukan titi da gwamnatinsa ta kammala a ranar Laraba.
- ’Yan Najeriya da ke Port Sudan na hanyar dawowa gida
- Sun kashe mai jego bayan karbar kudin fansarta sau biyu
A cewarsa, “A matsayinmu na gwamnati, akwai ayyukan da muka gada da muka kammala su; kamar yadda mu ma akwai ayyukan da gwamnati mai zuwa ta samu ba mu kammala ba; Kuma Allah Ne kadai Ya san gwamnatin da zan mika wa mulki, tsakanin NNPP da APC.”
Wasu na ganin akwai lauje cikin nadi a furucin nasa, wasu kuma na ganin borin kunya ne saboda zafin kayen da dan takarar jam’iyyarsa ta APC kuma mataimakinsa, Nasir Yusuf Gawuna ya sha a zabe.
Tuni dai Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) ta bayyana Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP a matsayin zababben gwamnan jihar Kano, har ta ba shi takardar shaidar zama zababben gwamna.
Amma kuma Jam’iyyar APC mai mulkin jihar ta garzaya kotu inda take kalubalantar ayyana Abba din da INEC ta yi a matsayin wanda ya ci zaben.
APC na ganin bai kamata INEC ta bayyana Abba a matsayin wanda ya yi nasara ba, domin kuwa kamata ya yi hukumar ta bayyana zaben a matsayin wanda bai kammala ba, saboda yawan kuri’un da aka soke a zaben ya haura tazarar kuri’un da ke tsakanin Abba da Gawuna.
Amma duk da haka a watan Afrilu, Gwamnatin Kano karkashin Ganduje ta kafa kwamitin mika mulki mai mambobi 17, da wasu kananan kwamitoci masu mambobi 100 da aka zabo daga hukumomi da ma’ikatun gwamnatin jihar.
Sai dai kuma a yayin da gwamnan ke kaddamar da wasu ayyukan hanyoyi a ranar Laraba, an ji shi yana cewa, Allah Ne Ya bar wa kansa masaniyar jam’iyyar da zai mika wa mulki a ranar 29 ga watan Mayu da muke ciki.