✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alkalin Kotun Koli ya mutu kwanaki 23 kafin ritayarsa

Wani alkalin Kotun Kolin Najeriya, Mai Shari'a Sylvester Ngwuta ya mutu a Abuja.

Wani alkalin Kotun Kolin Najeriya, Mai Shari’a Sylvester Ngwuta ya mutu a Abuja.

Majiyoyi a kotun sun tabbatar da cewar alkalin ya rasu ne da misalin karfe 2:00 na daren ranar Lahadi a gidansa dake Abuja.

Mai kimanin shekaru 70 a duniya, marigayi Mai Shari’a Sylvester ya rasu ne yana dab da yin ritaya daga aiki wanda aka tsara zai yi ranar 30 ga watan Maris bayan da ya cika shekaru 70 a duniya.

Marigayin dai na cikin alkalan da aka taba kamawa kuma aka tuhumesu da karbar rashawa a shekarar 2016 bayan wani samame da Hukumar Tsaron Farin Kaya ta DSS ta kai gidajensu.

Sai dai daga bisani a 2018 Babbar Kotun Tarayya dake Abuja ta wanke shi daga zargin da ake masa sannan ya ci gaba da shari’a a Kotun Kolin.