✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalin da ya dakatar da Ganduje ya janye umarnin

Alkalin da ya janye umarnin da ya bayar da farko na dakatar da Shugaban APC na Kasa Abdullahi Ganduje

Mai Shari’a Usman Na’abba na Babbar Kotun Jihar Kano ya janye umarnin da ya bayar na dakatar da tsohon gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, daga matsayinsa na Shugaban Jam’iyyar APC na Kasa.

Alkalin ya ba da umarnin ne kwanaki kadan hukuncin da ya yanke da farko bayan tsagin shugabancin APC na Mazabar Ganduje, karkashin jagorancin Haladu Gwanjo ya dakatar da tsohon gwamnan.

Amma a zaman kotun na ranar Litinin alkalin ya janye umarnin bisa bukatar lauyoyin Ganduje, wato L O Oyewo, A Falana da kuma J. Essiet.