Allah Ya yi wa Mai Shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye na Babbar Kotun Jihar Kwara rasuwa.
Alkali Sikiru Adeyinka Oyinloye ya rasu ne a ranar Asabar bayan fama da jinya, yana dan shekaru 58.
- Air Peace zai kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan kyauta
- NAJERIYA A YAU: Abin Da Ya Kamata Ku Sani Game Da Cutar Sankarau
A ranar Litinin ake sa ran gudanar da jana’izarsa kamar yadda addinin Musulunci ya tsara a mahaifarsa da ke Jihar Kwara.
A lokacin rayuwarsa, Mai Shari’a Sikiru Adeyinka Oyinloye, ya kasance alkali da ke nuna ba sani, ba sabo.
Ya yanke wa masu damfara ta intanet da dama hukunci tare da kwace kadarorinsu da suka hada da katafarun gidaje da motocin alfarma da kuma dubban daloli, ya damka wa gwamnati.
A shekara 2017 ya sanya tarar Naira biliyan hudu a kan kamfanin jaridar intanet ta Sahara Reporters da mai kamfanin, Omoyele Sowore, kan laifin wallafa labaran karya game da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Abubakar Bukola Saraki a 2015.
Ko da yake daga baya kamfanin ya daukaka kara.