✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkali ya janye daga shari’ar ’yan kungiyar Boko Haram

Mai Shari’a John Tsoho na Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ya janye daga shari’ar mutum takwas wadanda ake zargi da kasancewa kwamandojin kungiyar…

Mai Shari’a John Tsoho na Babbar Kotun Gwamnatin Tarayya da ke Abuja ya janye daga shari’ar mutum takwas wadanda ake zargi da kasancewa kwamandojin kungiyar Boko Haram.
Ana zargin su da kashe ’yan kasashen waje 11 a Arewacin Najeriya tsakanin shekarar 2011 zuwa shekarar 2013.
Wadanda ake zargi sun hada da Muhammad Usman wanda ake yi masa lakabi da Khalid Albarnawi wanda aka bayyana shi a matsayin shugaban kungiyar Boko Haram da suka ware mai suna Jama’atu Ansarul Muslimina Fi Biladis Sudan wacce ake kira ANSARU, sai Muhammad Sani da Abubakar Abdulrahman Habibu da Muhammad Bashir Saleh da Umar Muhammad Bello wanda ake kira Abu Azzan da Muhammad Salisu mai lakabin Datti da Yakubu Nuhu wanda ake kira Bello Maishayi da wata budurwa mai suna Halima Haliru.