✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Alkalai sun yi zanga-zanga bayan shafe shekaru 2 ba albashi

Alkalan kotunan majistare dake jihar Kuros Riba a ranar Litinin sun tare mashigar ofishin gwamnan jihar

Alkalan kotunan majistare dake jihar Kuros Riba a ranar Litinin sun tare mashigar ofishin gwamnan jihar dake Kalaba don nuna fushinsu bisa kin biyansu albashinsu na tsawon watanni 24.

Alkalan dai sun fito ne daga kananan hukumomi 18 na jihar suka kuma yi cincirindo dauke da kwalaye masu dauke da rubuce-rubucen neman hakkokin su.

Da yake jawabi a madadin sauran alkalan, Babban Alkalin jihar Solomon Abuo ya ce sun yanke hukuncin yin zanga-zangar ne saboda ita ce mataki na karshe da za su iya dauka.

Solomon ya ce duk da rashin biyan albashin sun ci gaba da aiki duk da rashin biyansu albashin.

Ya ce, “Akwai kotunan da muke jagoranta kuma muna aiki tukuru wajen ganin an sami adalci da zaman lafiya a cikin al’umma.

“Sai dai duk da haka gwamnan bai ga cancantar ya amsa kiraye-kirayenmu, wasikunmu da rokonmu ba.

“Yanzu haka muna da alkalai sama da 30 daga kananan hukumomi 18, abin takaicin kuma shine karamar hukumar da gwamnan ya fito ita ce ta fi yawan wadanda abin ya shafa, amma shi ko a jikinsa.

“Muna da iyali, muna da yara kuma suna karatu, yanzu ta kai ba ma iya biyan kudin makarantar yaran.

“Ko a bara sai da aka gurfanar da wani alkali a gaban wata kotun majistare saboda ya gaza biyan kudin hayar gidansu. Yawancinmu ba ma iya biyan haya, a gidajen ‘yan uwanmu muke zama.

“Addu’armu ita ce za a biya basussukanmu ba tare da bata lokaci ba, in kuwa ba haka ba, za mu ci gaba da wannan zanga-zangar kuma mu daina zaman kotuna har sai an biya mu hakkokinmu,’’ inji shi.