✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Alkalai sun kusa samun kariya daga gurfanarwa

Majalisa ta kammala karatu na biyu a kan kudurin dokar a zamanta na ranar Alhamis.

Majalisar Wakilai na gab da yin dokar kariya da za ta hana gurfanar da alkalan Kotun Koli da Manyan Kotunan Tarayya da na Jihohi a kotu har sai sun bar aiki.

Dan Majalisa Igariwey Iduma Enwo ya gabatar da kudirin, da nufin tabbatar da ‘yancin cin gashin kan bangaren shari’a da kuma tsare mutuncin alkalan daga bangaren zartarwa.

“Na yi amannar cewa bangaren shari’a ya cancanci samun kariya domin hana musu shisshigi daga wani bangare. Abin da ya dace da bangaren zartarwa shi ma bangaren shari’a ya dace ya samu”, inji shi.

Ya kara da cewa hakan zai ba kotuna cikakken ‘yancin sanya ido a kan kurakuran bangaren zartarwa kamar yadda kundin tsarin mulki ya kebe wa kowannensu ‘yanci da ayyukansa.

Honorabul Igariwey Iduma Enwo ya gabatar da kudirin ne domin neman gyaran fuska ga sashe na 308 da ya bayar da kariya ga shugaban kasa da gwamnoni da mataimakansu

Majalisar ta kammala karatu na biyu a kan kudurin dokar a zamanta na ranar Alhamis.