Gasar kwallon kafa ta kasar Spania (La Liga) ta nada tauraron finafinan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu a matsayin jakadanta a Arewacin Najeriya.
La Liga ta kaddamar da Ali Nuhu wanda furodusa ne kuma darekta a masana’antar Kannywood ne a taron farko na masoyanta wanda ya gudana a Kano, da hadin gwiwar gidan radiyon Arewa Radio.
- An cafke su suna yin fim din batsa a wurin ibada
- ’Yan Najeriya na shan wuya —Jega
- Buhari ko Obasanjo: Wa ya raba kan ’yan Najeriya?
Wakilin Aminiya ya ce tauraron finafinan ya ba wa masoyan La Liga a Arewacin Najeriya tabbacin kulla kyakkyawar dangantaka a tsakaninsu.
Da yake jawabi, Editan Wasanni na Coolfm/Wazobi/Arewa Radio, Sherif Abdallah ya ce Kano gida ce ga La Liga.
Ya ce yanzu aka fara kuma nan gaba abubuwan alheri za su zo wa Najeriya daga gasar, musamman a yankin Arewa.
“Mun kawo La Liga kusa da masoyanta. Yanzu aka fara kakar wasa kuma ba za mu yi kasa a gwiwa ba wajen kara dankon zumuncin da ke tsakanin gasar da masoyanta a Kano”, inji Abdallah.
Shi ma da yake jawabi a wurin taron, tsohon dan wasan kwallon kafa ta na kungiyar Super Eagles ta Najeriya, Mutiu Adepoju, ya yin farin cikin ganin La Liga na samun gagarumar kauna sakamakon goyon bayan daga Kanawa da sauran sassan Arewacin Najeriya.
Adepoju ya kara da kira ga masoya gasar da su kulla kyakkyawar alaka a tsakaninsu, sabanin mummunan adawa, duk da cewa kowannensu da kungiyar da yake bgoyon baya.