✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ali Nuhu ya samu mabiya miliyan 1 da dubu 500 a facebook

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya gode wa masoyansa sakamakon samun mabiya miliyan daya da dubu 500 a shafin sada zumunci na facebook. A…

Shahararren jarumin fina-finan Hausa, Ali Nuhu ya gode wa masoyansa sakamakon samun mabiya miliyan daya da dubu 500 a shafin sada zumunci na facebook.

A cikin wani sako da jarumin ya fitar a ranar Alhamis din makon jiya, bayan ya sanya wani hoto da yake sanye da fararen kaya, ya kuma yi tsalle ne, ya gode wa masoyan nasa.

A tattaunawarsa da Aminiya ya bayyana ya yi farin ciki mara misaltuwa da ya samu adadin yawan mabiyan, inda hakan ya nuna masa mutane suna gamsuwa da abubuwan da yake yi.

Ya ce, “Idan har da a ce abin da nake yi ba ya gamsar da su, to da raguwar masoyana za su rika yi ba karuwa ba, ka ga hakan ya nuna mini ina kan turba mai kyau, kuma hakan ya kara mini kaimi ne, don in ci gaba da yin abubuwan da zai burge su.”

Ya ce ba don masoyansa ba to ba zai kai matsayin da yake kai ba, don haka ba shi da hakikanin dadadan kalmomin da zai yi amfani da su wajen nuna godiyarsa gare su da kuma fahimtar da su amfaninsu gare shi.

Ya kuma yi wa masoyansa albishir din ba zai yi kasa a gwiwa wajen ci gaba da burge su ba, domin a yanzu shirye-shiryen sun yi nisa wajen fara daukar sabon fim din kamfaninsa na FKD Production mai suna ‘Abota’, inda jaruma Nafisa Abdullahi za ta jagoranta.

Ya kuma yi kira ga ’yan kallo da kada su yi kasa a gwiwa wajen sanar da shi kura-kuran da suka ga yana aikatawa ba tare da ya sani ba, domin dan Adam tara yake bai cika goma ba.