Fitaccen jarumin Fina-finan Hausa na Kannywood, Ali Nuhu, ya janye karar da ya shigar gaban kotu na kalubalantar jaruma Hannatu Bashir.
Idan za a iya tunawa a makon jiya ne jarumi Ali Nuhu ya maka Hannatu Bashir a gaban Kotun Majistare da ke zamanta a Nomanslan a Jihar Kano inda ya zarge ta da cin zarafinsa.
- Kisan Ummita: An sake gurfanar da dan China a kotu
- Yadda ambaliyar ruwa ta haifar da tsadar shinkafa a bana
Tunda farko takaddama ta taso ne a tsakanin jaruman biyu bayan Ali Nuhu ya gaza halartar wurin daukar wani fim din da Hannatu ta shirya, lamarin da ya bata ran jarumar har ta aika masa sakon bakaken maganganu, shi kuma ya maka ta a gaban kotu.
Duk da cewar jaruma Hannatu ta musanta batun cin zarafin Alin inda ta ce maganganun da ya aiko mata a nasa sakon sun fi nata zafi amma ba ta mayar masa da martani ba.
“Abin da ya fi bata min rai a wannan lamarin shi me da kansa Ali Nuhu ya zabi ranar da za a dauki fim din wato ranarr 10 ga watan Oktoba sai dai bai halarci wurin daukar fim din ba kamar yadda ya yi alkawari haka kuma bai bayar da uzurin yin hakan ba.
“Hakan ya sa na rubuta masa sakon ta wayarsa inda kuma ya aiko min da maganganun da suka fi nawa zafi. Sai dai ban ba shi amsa ba duba da cewa shi babba ne ya sa na bar maganar.”
A zaman kotun baya, jaruma Hannatu ba ta halarta kotun ba lamarin da ya sa kotun ta bayar da umarnin jarumar ta halarci zama na gaba da kanta ba wai ta tura lauya ba.
A zaman ranar Alhamis, Hannatu ta hallara inda lauyan Ali Nuhu ya bayyana wa kotun cewa wanda yake wakilta ya janye karar da ya shigar biyo bayan sulhun da ake kokarin yi a tsakanin jaruman biyu.
Ita ma a nata bangaren wacce ake kara jarumar, wacce ta je kotun tare da lauyoyinta uku ta amince da batun janyewar.
Tunda farko sai da alkalin kotun, Mai Shari’a, Aminu Gabari, ya nemi sanin dalilin jarumar na rashin halartar zaman kotun na baya, ba tare da ta sanar cewa ba ta da lafiya ne a lokacin, hakan ya sa kotun ta yi mata afuwa.
Daga nan kotun ta hori dukkanin bangarorin biyu da su ci gaba da zaman lafiya da juna.