Ali Kachalla shi ne jagoran ’yan bindigar da ya kitsa ya kuma jagoranci kakkabo jirin yakin Rundunar Sojin Sama ta Najeriya a Jihar Zamfara.
Duk da cewa ba a san shi sosai ba, bincikenmu ya gano cewa ’yan bindiga akalla 200 ne suke karkashinsa, kuma su ne suka addabi garin Dansadau na Jihar Zamfara a baya-bayan nan, inda suka kona motar yaki.
- ’Yan bindiga na bore kan sauke sarki a Zamfara
- Daliban FGC Yauri 2 sun tsere daga hannun ’yan bindiga
A ranar 18 ga watan Yuni ne ’yan bindiga suka harbo jirgin yaki, wanda Rundunar Sojin Saman ta ce an bude masa wuta ne a hanyarsa ta dawowa daga yakar ’yan bindiga a iyakar Jihar Zamfara da Jihar Kaduna.
Har yanzu ba a bayyana hoto ko bidiyon jirgin ba, amma mun kawo rahoton yadda matukin jirgin, Flight Lieutenant Abayomi Dairo, ya yi saukar lema, daga bisani ya yi ta sanda har ya shiga wani kauye ya boye, daga baya mutanen kauyen suka taimaka masa ya je wani sansanin sojoji.
Hukumomi ba su bayyana ainihin wanda ke da hannu a harbo jirgin sojin ba, amma bincikenmu ta majiyoyin tsaro da wasu mazauna yankin sun bayyana mana cewa Ali Kachalla da yaransa ne suka harbo jirgin.
Mun gano cewa Ali, wanda ba a fiye jin sunansa a cikin ’yan bindiga ba, yana zaune tare da yaransa ne a cikin Dajin Kuyambana wanda ya ratsa jihohin Zamfara da Kebbi da Kaduna da kuma Neja.
Mazauna a yankin Dansadau a Jihar Zamfara sun dade da sanin shi domin ya addabe su da hare-hare, musamman a baya-bayan nan, kuma yana yawan yi wa sojoji kwanton bauna.
Wane ne Ali Kachalla
Ali matashi ne mai shekara 30 da wani abu haifaffen kauyen Madada ne da ke kusa da garin Dansadau.
Wani wani wanda ya san yankin a ce a halin yanzu Ali Kachalla da yaransa sun yi sansani a gabar Kogin Goron Dutse, wanda ya ratsa tsakanin iyakokin jihohin Kaduna da Zamfara. Kogin na da nisan kilomita 25 daga Dansadau.
“Akwai bukkoki da yawa a sansanin nasa ta bangaren Birnin Gwari, garken shanunsa da yaransa masu dauke da muggan makamai ke kula da su kuma na ta bangaren Jihar Zamfara.
“Yanzu haka akwai yaransa a kauyukan Dandalla da Madada da kuma Gobirawa Kwacha da ke Kudu Maso Yamma da garin Dansadau kuma ’yan bindiga na yin yadda suka ga dama a kauyukan,” inji majiyar da ta bukaci a boye sunanta.
Ana kwatanta Ali Kachalla da yaransa cewa marasa tsaro ne kuma sun sha kai wa jami’an tsaro hari; Ana kuma ganin yaran nasa sun fi na yawancin gungu-gungun ’yan bindiga yawa.
A baya-bayan nan ne Ali Kachalla ya tsananta kai wa garin Dansadau hari saboda zargin mutanen garin sun taimaka wa matukin jirgin yakin da Alin ya so kamawa da ransa. Yana kuma jin haushi cewa mutanen garin sun dakile hanyar kai wa ’yan bidiga kayayyakin bukata.
A wani hari da suka kai, yaran nasa sun kona wata motar yaki bayan sun fatattaki jami’an tsaro da aka girke.
“Garin Dansadau ya ga ta kansa a hannun Ali da yaransa saboda mutanen garin sun hana ’yan tireda sayar masa da kayan abinci.
“Amma duk da haka akwai miyagun mutane da ke kai musu burodi da lemon kwalba da sauran kayayyaki a cikin dajin,” inji wata majiya.
A baya-bayan nan ne mazauna ganin suka dauki matakin dakile duk hanyoyin kasuwanci da ’yan bindigar.
Jami’an tsaro da taimakon mutanen garin sun kuma matsa kaimi wajen kamo masu kai wa ’yan bindiga bayanai.
A makon jiya mun kawo rahoton yadda sojoji suka damke mutum 30 masu yi wa ’yan bindigar leken asiri, ciki har da wata mace.
Daya daga cikin mutanen da aka kama ya kona kansa bayan ya yi kokarin kwace bindigar wani soja a sansanin sojojin da ake tsare da su.
Gawurtarsa bayan kashe Buharin Daji
Ali na daga cikin yaran tsohon shugaban ’yan bindiga, Buhari Daji da suka fara tashe bayan mataimakin Buharin Dajin, Dogo Gide ya bindige shi.
Ali da Dogo abokan juna ne amma ba su hade ba, kowannensu ya hada yaransa yana addabar mutane kamar tsohon uban gidan nasu.
Ali da tawagar sun tsaya a yankin Zamfara, shi kuma Dogo Gide yana tafiya daga wuri zuwa wuri yana addabar jama’a.
Majiyoyin sun shaida mana cewa baya ga tsoffin yaran Buharin Daji da suka koma karkashin Ali, ya kara daukan sabbin yara.
“Akwai yara Hausawa da yawa sa suka shiga gungunsa, cikinsu har da ’yan garin Dansadau, suna tare da shi a cikin daji,” inji majiyar.
A yayin da ba a fiye ganinsa ba, Kachalla da yaransa sun sha dandana kudarsu a hannun jami’an tsaro.
A bayan nan kuma an kashe yaransa kusan 30 a wani dauki-ba-dadi tsakanin yaransa da yaran Malam Babba — shugaban kungiyar Ansaru a yankin Arewa Maso Yamma.
Sagir Kano Saleh da Abdulaziz Abdulaziz da Shehu Umar, Gusau.