Jimillar kuɗaɗen albashi da alawus-alawus din da ake biyan sanatocin Najeriya a duk wata ya haura Naira biliyan biyu.
Kawo yanzu dai albashi da alawus-alaw din sanatoci 99 da ke majalisar aka gano, banda na shugabanninta su 10.
A ranar Laraba Sanatan Kano ta Kudu, Abdulraham Suleiman Kawu Sumaila, ya sanar cewa a duk wata ana biyan sa Naira miliyan 21.
“Kowane sanata yana karɓar Naira miliyan 21 a duk wata a matsayin kudaden gudanar da ofishinsa”, in ji Sanata Kawu Sumaila a hirarsa da BBC Hausa a ranar Laraba.
- Ana neman ƙwace filin masallacin ’yan Arewa don gina dandalin baɗala a Abiya
- NAJERIYA A YAU: Shin Matasa Sun Shirya Karɓar Ragamar Shugabanci A Najeriya?
Sai dai ya ce bai san nawa ake biyan Shugaban Majalisar Dattawa da mataimakinsa da ragowar mutum takwas da ke jagorantar majalisar ba.
Idan aka ninka miliyan 21 sau 99, jimilla shi ne Naira biliyan biyu da miliyan 79.
Kawo yanzu dai ba a da san haƙiƙanin abin da ake biyan shugabannin majalisar ba.
’Yan majalisa da dama sun bayyana cewa ba su da masaniyar albashi ko adadin hadiman da ke ofisoshin jagororin majalisar.
Shugabannin majalisar guda 10 masu ci dai so ne:
- Shugaban Majalisar Dattawa – Sanata Godswill Akpabio
- Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa – Sanata Barau Jibril
- Shugaban Masu Rinjaye – Sanata Opeyemi Bamidele.
- Mataimakin Shugaban Masu Rinjaye – Sanata Lola Ashiru
- Babban Mai Tsawatarwa – Sanata Tahir Monguno
- Mataimakin Babban Mai Tsawatarwa – Sanata Nwebonyi Peter Onyeka
- Shugaban Marasa Rinjaye – Sanata Abba Moro
- Mataimakin Shugaban Matsa Rinjaye – Sanata Akogun Lere Oyewumi
- Mai Tsawatarwan Matsa Rinjaye – Sanata Ngwu
- Mataimakin Mai Tsawatarwan Marasa Rinjaye – Sanata Rufai Hanga.
Kokarinmu na samun ainihin alƙaluman kuɗaɗen da ake biyan shugabannin majalisar daga mai magana da yawun Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, a ranar Laraba ya gagara.
Sanatan ban amsa kiran Wakikinmu ba, kuma bai amsa rubutaccen sakon da aka tura masa ba.
A baya-bayan nan dai ana yi ta ce-ce-ku-ce game da albashi da alawus din ’yan majalisar dokoki kasar nan.
Tsohon sanata su Shehu Sani, da tsofaffin ’yan majalisar wakilai, Muhammad Sani Zoro da Sergius Ogun, abin ya fada cewa shi ne albashin sanatocin Majalisa ta 10 ya sha bamban da na ɗan uwansa.
Su kuma kalubanci sanatocin na yanzu da su fito su bayyana wa duniya ainihin abin da ake biyan su a duk wata.
Ogun, wanda dan majalisar tarayyar Esan ta Arewa maso Gabas/Esan ta Kudu maso Gabas ne daga 2015 – 2023, ya ce miliyan N8.5 ake biyan kowane dan majalisar a matsayin kudin gudanar a wata a zamaninsu.
Sani Zorro, wanda tsohon dan majalisar tarayyar Gumel/Maigatari/Sule Tankarkar/Gagarawa daga Jihar Jigawa ne daga 2015 to 2019, ya ƙalubalanci na yanzu su fito su bayyana abin da ake biyan su.
Shehu Sani wanda Sanatan Kaduna ta Tsakiya ne daga 2015-2019, ya ce ana biyan kowane sanata miliyan 13.5 a duk wata a matsayin kudin gudanarwa, baya ga albashin Naira 750,000 da Hukumar Tsara Alabshi ta Ƙasa (RMAFC) ta tsara musu.
A baya-bayan nan, tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo ya zargi ’yan majalisar dokoki ta kasa da yi wa kansu albashi, wanda ya ce, “abin Allah wadai ne.”
Amma a martaninsa ga Obasanjo, kakakin Majalisar Dattawa, Sanata Yemi Adaramodu, ya ce abin da hukumar RMAFC ta tsara musu kawai ake biyan su.
Sai dai kuma a na sa bangaren, lokacin da yake raddi ga Shehu Sani, Shugaban Hukumar RMAFC, M. B. Shehu, ya bayyana cewa tsira albashin wata na kowane sanata shi ne N1,063,860.
Sai dai sanarwar da ya fitar a ranar Talata ta yi karin haske da cewa hukumar ba ta da ikon tabbatar da aiki da abin da ya tsara na alabshi.
Sanarwar ta ci gaba da cewa, “amma Majalisar Dokoki ta Kasa tana kokarin warware wannan matsala.”
Sai dai kuma, abin da Sanata Kawu Sumaila ya bayyana ya saba da abin da shugaban na RMAFC ya sanar. A cewar Kawu Sumaila, “tsurar albashin sanata bai kai miliyan daya ba a wata, idan aka cire abubuwan da aka yankewa sai ya koma kimanin N600,000.
“Amma duk sanata yana karɓar miliyan 21 a kowane wata a matsayin kudaden gudanar da ofishinsa,” in ji shi.
Ya bayyana cewa miliyan 21 din ya haɗa kuɗaɗen sun kunshi na sayen jarida, tafiye-tafiyen cikin gida, da dai sauransu.