Kwamitin daidaita albashin da gwamnatin tarayya ta kafa kwanan nan kan sabon mafi karancin albashin N70,000 ya kammala aikinsa, kuma bangarorin sun rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Kimanin makonnin biyu ke nan da gwamnatin ta kaddamar da kwamitin mai mambobi 16 bisa tanadin dokar mafi karancin albashi na kasa na Naira 70,000, wanda shugaba Bola Tinubu ya amince da shi.
Shugabar kwamitin kuma shugabar ma’aikatan gwamnatin tarayya, Misis Didi Walson-Jack, ce ta kaddamar da kwamitin a madadin shugaban kasa bayan amincewarsa da sabon mafi karancin albashin ma’aikatan tarayya daga N30,000 zuwa N70,000.
Da take magana bayan rattaba hannu kan yarjejeniyar a Abuja, Misis Walson-Jack, ta ce “Kungiyoyin kwadago da bangarorin gwamnati sun amince da gyare-gyaren albashi bisa sabon mafi karancin albashi na N70,000.”
Walson-Jack a cikin wata sanarwa mai dauke da sa hannun Mrs Eno Olotu, ta kara da cewa dukkan mambobin kwamitin sun sanya hannu kan yarjejeniyar, don haka aikin ya kammala da mika kwafin ga wakilan bangarorin biyu.
Ta ce za a mika kwafin yarjejeniyar da aka rattabawa hannu ga gwamnatin tarayya domin daukar mataki na gaba.
A nasa bangaren, shugaban majalisar hadin gwiwa ta kasa, Kwamared Benjamin Anthony, wanda ya wakilci bangaren kungiyar kwadago ya yabaw a shugabar ma’aikatan tare da nuna gamsuwa da aikin kwamitin.