Kamfanin jiragen sama na Air Peace ya kori matuka jirginsa kan rashin amincewa da rage musu albashi.
Kamfanin ya yi yunkurin rage kashi 80 cikin dari na albashin matuka jirgin saboda rashin samun ciniki da annobar COVID-19 ta haifar, amma suka ki yarda.
Rashin amicewarsu da matakin ya haifar rashin jituwa tsakaninsu da hukumar kamfanin na Air Peace.
Wakilinmu ya ruwoito cewar kamfanin ya nemi rage albashin ne bayan dawowa daga zama wata hudu babu aiki, kasancewar ya hagon ba zai iya biyan su yadda aka saba ba saboda rashin fasinjoji.
Wata majiya ta ce babu hanyar da kamfanin bai bi ba domin direbobin jirgin su fahimci matsalar da ya shiga sakamakon COVID-19 amma suka cije.
Majiyar ta ce kamfanin ya sallami rabin matuka jirgin ne saboda rashin cimma matsaya kan rage albashin.
Wata majiyar kuma ta ce an riga an raba wa direbobin jirgin takardun sallamar su daga aiki.
Da wakilinmu ya kira mai magana da yawun kamfanin, Stanley Olisa, bai ce hakan ya faru ba ko kuma bai faru ba, amma ya ce zai fitar da bayanin kamfanin a rubuce.