Fitaccen mawakin Hausar nan, Aminu Ala tare da wasu abokan tafiyarsa sun tsallake rijiya da baya a wani hatsarin mota da ya rutsa da su.
A wani sako da ya wallafa a shafinsa na Instagram, mawakin ya ce Allah Ya takaita hatsarin a kan abin hawansu ba tare da wani daga cikinsu ya jikkata ba.
- Wike ya kara yawan hadimansa zuwa mutum 200,000
- Kotu ta ba da umarnin kwace kadarorin Sanata Ekweremadu
Ala ya wallafa hotunan yadda motarsu ta kwararrabe sakamakon hatsarin.
Duk da dai sakon bai nuna takamammen inda hatsarin ya auku ba, amma mawakin ya jadadda godiyarsu ga Allah da Ya tsirar da su a hatsarin.
Daruruwan masoya sun bi mawakin zuwa shafin nasa inda ya wallafa sanarwar hatsarin, inda suka jajanta masa tare da yi masa fatan Allah Ya kare gaba.