A kwanakin baya ne ministan ayyukan gona Mista Audu Ogbe ya bayyana cewa alalen da aka dafa a cikin leda yana iya zama guba ga duk wanda ya ci saboda sinadrin da ke cikin kedar yana shiga cikin alalen a sakamakon zafin da ledar ta dauka.
Mista Audu Ogbe ya ci gaba da cewa alalen da aka dafa a cikin ganye ne ba shi da wata illa, domin babu wani sinadari mai cutarwa a tattare da ganyen wanda a sanadiyyar daukar zafi zai shiga cikin alalen da aka dafa har ya cutar da wanda ya ci.
Aminiya ta yi kokarin samun ministan domin ya yi karin bayani amma haka ya ci tura, saboda haka sai ta tuntubi masana a fannin kiwon lafiya da kuma kimiyyar sinadarai domin su yi karin bayani game da wannan furuci da ministan gona Audu Ogbe ya yi.
Akwai yiwuwar alalen ya cutar da lafiya
– Dokta Mahmud Salihu.
Dokta Mahmud Salihu likita ne a fannin lafiyar iyali (Family Medicine), a asibitin koyarwa na Jami’ar Ahmadu Bello da ke Zariya, Aminiya ta tuntube shi domin jin ta bakinsa game da wannan al’amarin.
Aminiya: Dokta muna son karin bayani ne a game da wani bayani da ministan harkar noma Audu Ogbeh ya yi inda ya ce alalen da aka dafa a cikin leda yana da illa ga lafiya?
Dokta: Gaskiya ni dai a kimiyance ban taba ganin wani bayani kamar haka ba, amma ana fadin haka, duk da cewa ban san wani binkice game da hakan ba. Amma yadda ake bayanin yake shi ne, tun da dai a kamfani idan za a hada ledojin ana sanya sinadarai (chemicals) wurin sarrafa su, to masu bincike a kan muhalli suna ganin cewa duk wani abu da ake sawa a cikin leda, kamar abinci, sannan kuma aka dora su a kan wuta, to su wadannan sinadaran da ake sawa a jikin ledodin domin ya kara musu karko, idan sun ji wuta sukan shiga cikin abincin, duk da cewa ban taba ganin wani bincike a kan haka ba, domin sai an gwada shi alalen sannan za a ga cewa lallai akwai wadannan sinadaran da ake sanyawa a cikin ledodin, idan har sun shiga din, a hankali wadannan sinadarin sukan taru a jikin mutum bayan wani lokaci mai tsawo, domin cutar kansa (cancer) da rashin lafiya ba a lokaci guda suke farawa ba, za su taru har su kai wani matsayi da za su iya jawo matsaloli ga lafiya. A kan ce sukan shafi koda da hanta da wadansu bangarorin jikin mutum.
Aminiya: Ke nan kamata ya yi a rika sanya alalen a cikin ganye ba a cikin leda ba?
Dokta: Su kuma masana abinci sun ce alalen da aka sanya a cikin ganyen ayaba aka dafa, suna ganin shi ganyen ayaban ba shi da wadansu sinadarai masu illa, sannan kuma suna ganin yana kara wa alalen dandano da kamshi, domin wadansu sinadaran da ba su da illa suna shiga cikin alalen daga cikin ganyen. Domin haka wadannan masanan suna ganin alalen ganye ya fi wanda aka sanya a cikin leda, domin hatta ma ruwan da ake sanya wa a cikin robobi idan suka dade a cikin rana su ma suna iya yawo wadansu matsalolin. Kawai dai abin da masana suke nufi shi ne, sinadaran da ake sanyawa a cikin ledodin a gaskiya suna da illoli masu yawa ga lafiyar mutum.
Aminiya: Saboda haka gara alalen ganyen ke nan?
Dokta:A gaskiya gara wanda aka sanya a cikin ganye, tunda dai shi na ganyen ba a cewa akwai wani illa, amma shi na leda ana cewa akwai illoli.
Aminiya: Bayanan yawancinsu hasashe ne ke nan?
Dokta: Gaskiya, domin babu wani bincike da ya tabbatar da hakan, saboda idan ana so a tabbatar sai an dauki samfurin shi alalen an je dakin gwaji an duba an ga shin wadannan sinadaran da ake hada ledodin da su akwai su a cikin alalen, idan aka tabbatar akwai su, sai a ce to za su taru a cikin alalen, domin haka sai a ce lallai idan ana hada alalen da leda za su taru kadan-kadan har su jawo illa ga lafiyar mutum.
Ana iya kamuwa da cutar kansa – Farfesa Abdussalami
Farfesa M.S. Abdussalami Mataimakin farfesa ne da ke koyarwa a Sashin koyar da ilmin halittu (Biological Science) a Kwalejin Horar da kananan Hafsoshin soja (NDA) da ke Kaduna, ya yi bayanin yadda lamari yake a kimiyance kamar haka:
Aminiya : mene ne gaskiyar magana a kan cewa idan an dafa alale a cikin leda yana jawo illoli ga lafiya?
Farfesa: Matsalar ita ce, akwai wani sinadari mai suna Diodine wanda yake fita daga cikin leda idan an kona ledar, sannan kuma idan ana sarrafa leda a kamfani, akwai wadansu sinadarai da ake kira plasticizers wadanda ake sanyawa a lokacin sarrafa ledar, biyu daga cikin wadannan sinadaran sune bisphenol, wanda aka fi sani da BPA, da kuma phalates, wadannan sinadaran ana kara su ne domin su kara wa ledar karfi ko kuma aminci. To idan aka sanya abinci a cikin wannan ledar sannan kuma aka dora a kan wuta, wadannan sinadaran za su iya fitowa daga cikin ledar su shiga cikin abincin, wanda zai jawo matsaloli masu yawa ga lafiya. Sannan kuma sinadaran sun fi shiga cikin abinci wadanda masu maiko ne. To idan ana so a kare faruwar hakan, idan za a sanya abinci a cikin leda, dole a tabbatar abincin bai taba ledar ba kai tsaye, domin suna haduwa ledar za ta iya sako sinadaran da ke cikinta su shiga cikin abincin, musamman idan an dora a kan wuta. Sannan kuma ya kamata idan an hada wadannan ledojin, a rika gwada su, sannan a bayyana ko za su iya cutarwa ko ba za su cutar ba. Ina ganin idan aka lura da wadannan abubuwan za a iya rage matsalar da za a iya samu. Sannan ya kamata ayi amfani da ganye wurin dafa alalen, kamar yadda wadansu suke fada, sannan kuma za a iya yin amfani da wani nau’in kyalle da ake kira “wad paper” domin ba shi da wani illa ga lafiya.
Aminiya: Kamar wadanne irin cututtuka za a iya kamuwa da su a sanadiyar wannan sinadaran ?
Farfesa: danWasu gabobi da yawa suna iya kamuwa da cutar kansa, wadanda ake ci gaba da bincike a kansu a yanzu.
Masana a fannin likitanci na jami’ar Harbard sun yi bincike sosai a kan wannan sinadaran, inda suka nuna cewa wadannan sinadaran suna iya yin kamanceceniya da wadansu sinadaran jikin mutum masu suna hormones, sai jiki ya dauke su a matsayin asalin sinadarin da yake bukata, wanda hakan zai jawo wa jikin matsaloli da yawa. Hakan ne ya sa ake kiransu da suna “endocrine disrupters.”
Aminiya: To kamar mene ne zai iya faruwa idan wadannan sinadaran suka yi kama da sinadaran jiki a cikin jikin mutum?
Farfesa: Ya zama ke nan za a samu matsala a gabar da suka shiga, sannan kuma tun da wadannan sinadaran suna jawo kansa, duk gabar da ta dauke su a matsayin abin da take bukata, domin sun yi kama, gabar za ta zama ta samu kansa ke nan.
Ba mu san haka ba – Madam Salomi
Madam Salomi Nkocha, wacce take sayar da abinci a Abuja ta ce ba ta san cewa leda tana da illa ga abinci ba. Ta ce idan ta yi abinci tana rufe shi ne da leda lamar yadda taga ana yi, domin kada ya yi saurin yin sanyi. Sannan ba ta san ko dafa alale da leda yana da wata illa ba.
Alalen da aka dafa a leda yana iya zama guba – Masana
A kwanakin baya ne ministan ayyukan gona Mista Audu Ogbe ya bayyana cewa alalen da aka dafa a cikin leda yana iya zama guba ga…