Wani maniyyacin Jihar Kano da bai samu tashi a jirgin karshe ba zuwa kasar Saudiyya b ranar Alhamis ya ce zai yi Aikin Hajjinsa na bana a sansanin horar da alhazai da ke Jihar.
Maniyyacin, mai suna Malam Jibrin Abdu, wanda ya fito daga Karamar Hukumar Gezawa da ke Jihar dai ya dauki hankulan jama’a ne lokacin da aka gan shi sanye da harami, inda ya ce shi tuni ya fara Aikin Hajjin nasa a Kano.
- Kotu ta daure sojan karyar da ke kwaikwayon sa hannun Buhari shekara 7
- Jirgin karshe ya tashi ya bar shugaban hukumar alhazan Kano da wasu maniyyata 745 a kasa
“Ai ni tuni na fara Aikin Hajjina, tun da muna da duk abubuwan da ake zuwa Saudiyya a yi a nan Kano, kuma zan dawo na karasa. Wannan ba shi ne karo na farko ba, kuma ba zai zama na karshe ba,” inji maniyyacin, kamar yadda ya shaida wa Aminiya.
Ya ce har gonarsa ya sayar saboda ya biya kudin Aikin, amma son zuciyar wasu shugabanni ta hana shi tafiya.
Ban da Malam Jibrin Abdu dai, Suwaiba Sani tare da sauran maniyyatan sun yi ta yin tofin ala-tsine tare da yin Allah-wadai da duk wanda ya yi silar jefa su a halin da suka tsinci kansu.
Idan za a iya tunawa, Aminiya ta rawaito muku yadda jirgin karshe ya bar shugaban Hukumar Jin-dadin Alhazai na Jihar Kano, Abba Danbatta, wasu Daraktocin hukumar da wasu maniyyata 745 a kasa, inda ba za su sami damar sauke farali ba a bana.
Jirgin na kamfanin Azman, wanda ya tashi wajen misalin karfe 3:40 na yammacin Alhamis, ya bar maniyyatan ne duk da karin wa’adin da kasar Saudiyya ta yi wa Najeriya.