Oba Lamidi Adeyemi, Alafin na Oyo kuma babban basarake a kasar Yarbawa, ya riga mu gidan gaskiya.
Oba Lamidi Adeyemi, ya rasu ne bayan shafe shekara 52 a kan karaga, wanda ya mayar da shi mutum mafi dadewa a kan sarautar ta Alafin na Oyo.
- ‘Ya kamata a binciki duk wanda ya sayi fom din takarar APC N100m’
- A Kannywood ne zaka ga ’ya’yan da iyayensu suka kasa kula da su – Sarkin Waka
Hadimin basaraken kan yada labarai, Bode Durojaiye, ya tabbatar wa Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya cewa, “Won ti ku” (wato sarkin ya rasu, cikin harshen Yarbanci) ta wayar tarho.
Basaraken mai shekara 83, ya rasu ne da miasalin karfe 11 na dare, kafin wayewar garin Asabar, a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Afe Babalola da ke Ado-Ekiti, Jihar Ekiti.
Majiya mai tushe ta shaida wa Aminiya cewa a safiyar Asabar din aka isar da gawar mamacin garin Oyo.
Majiyar ta ce tuni babban dansa, Yarima Tunde Adeyemi, tare da ’yan uwansa suka tarbi gawar a yankin Idi-Igba, kuma fadarsa ta fara shirye-shiryen jana’iza.
Sanawar gwamnati
Sakamakon rasuwar tasa, ragamar gudanar da harkokin dafar za ta koma hannun Shugaban Oyomesi, Basorun na Oyo, Babban Cif Yusuf Akinade Ayoola, har a nada sabon Alafin.
Ana san ran nan gaba Gwamnan Seyi Makinde na Jihar Oyo zai fitar da sanarwar rasuwar bayan samun bayani daga Basorun a safiyar Asabar.
Rasuwar sarakuna uku a wata biyar
Marigayi shi ne Alafin na uku da ya jagoranci Masarutar Oyo daga zuriyar gidan Sarautar Alowolodu.
Oba Lamidi Adeyemi shi ne babban basarake na uku a Masarautar Oyo da ya rasu cikin wata biyar da suka gabata.
A ranar 12 ga Disamban 2021, Soun na Ogbomoso, Oba Jimoh Oyewumi, ya riga mu gidan gaskiya.
Daga baya Olubadan Saliu Adetunji ya kwanta dama a ranar 2 ga Janairu, 2022.