Kungiyar Al-Shabaab ta kai hari a filin saukar jiragen sama na Mogadishu babban birnin Somaliya.
Harin na Mogadishi ya auku ne a yankin da ofisoshin Majalisar Dinkin Duniya da na jakadanci da kuma sansanin Dakarun Tabbatar da Zaman Lafiya na Tarayyar Afirka AMISOM suke.
- Shekara 30 Atiku na neman kujerar shugaban kasa
- Fiye da rabin yara a Ukraine sun koma ’yan gudun hijira – UNICEF
Shaidun gani da ido sun ce an yi musanyar wuta a cikin filin saukar jiragen saman a artabun da aka kwashe sa’o’i ana yi a sa’ilin da wasu mutanen guda biyu dauke da makamai suka kai harin.
Akalla an kashe sojin gwamnatin daya yayin da wasu da dama suka jikkata, sai dai kawo yanzu ba a da masaniya kan ko dakarun gwamnatin sun yi nasarar murkushe ’yan ta’addar.
BBC ya ruwaito cewa akalla mutum 15, ciki har da wata ’yar majalisar kasar Somaliya sun halaka, bayan da wasu ’yan kunar bakin wake suka kai tagwayen hare-hare a garin Beledweyn na tsakiyar kasar.
Firaminista Mohamed Hussein Roble ya bayyana kashe Amina Mohamed Abdi a matsayin “kisan gilla”.
Haka kuma shugaban kasar Abdullahi Farmajo ya aika da sakonsa na ta’aziyyar ta Twitter.
Cikin mamatan akwai tsohon dan majalisa Hassan Dhuhul da wasu sojojin Somaliya.
Kafofin yada labarai a yankin na cewa yawan mamatan na iya zarce alkaluman wadanda aka sanar a yanzu.
Babbar tashar talabijin ta Somaliya ta wallafa wasu hotuna na wadanda aka kashe yayin harin.
Kungiyar Al-Shabaab ta dauki alhakin kai hare-haren – wadanda aka kai a biranen Mogadishu da tsakiyar Beledweyne.
A shekara ta 2011 sojojin rundunar tabbatar da zaman lafiya na AMISOM suka kori Al Shebab da ke yakar gwamnati daga Mogadishu.
Sai dai har yanzu tana rike da yankuna da dama na karkara, kana tana ci gaba da kai hare-hare kan cibiyoyin gwamnati da na sojoji.