Gwamnatin Somaliya ta sanar da cewa daya daga cikin manyan wadanda aka assasa kungiyar al-Shabaab da su, Abdullahi Nadir ya rasu bayan an kashe shi a ranar Asabar a yankin Juba na kasar.
Rahotanni sun ce dakarun hadin gwiwa da suka hada na gwamnatin Somalia da na ketare ne suka kashe Mista Nadir wanda aka fi sani da Abdullahi Yare.
- Satar Mutane ta ragu da kashi 28 a watan Agusta —Rahoto
- Matashi ya harbe kaninsa yayin gwada maganin bindiga
Ma’aikatar Watsa Labarai ta kasar ta bayyana cewa, Mista Nadir ne shugaban bangaren watsa labarai na farfaganda na al-shabaab.
An kashe Abdullahi Nadir, babban jagoran ’yan ta’addar al-shabaab, wanda gwamnatin Somaliya ke nema ruwa a jallo, a wani samame da aka kai,” in ji Ma’aikatar Yada Labaran.
Tuni dama Amurka ta saka ladan dala miliyan uku ga duk wanda ya kai mata Mista Nadir.
Kafafen watsa labarai na kasar dai na cewa jirgi mara matuki ne ya kashe Mista Nadir a wani hari da ya kai.
Ma’aikatar ta ce an gudanar da farmakin na hadin gwiwa da sojojin Somaliya da kuma takwarorin tsaron kasa da kasa suka gudanar a kauyen Haramka da ke Kudancin yankin Juba ta Tsakiya.
Tun a shekarar 2007 ne kungiyar al-Shabaab wadda ake alakantawa da al-Qaeda ta kaddamar da kazamin yaki kan gwamnatin Somaliya da dakarun kasa da kasa.
Har yanzu kungiyar al-Qaeda ba ta ce uffan ba game da mutuwar Nadir.