Kungiyar al-Shabaab ta kashe kimanin mutane 20 a Somaliya tare da kone ababen hawan da ake amfani da su wajen jigilar kai tallafin abinci a tsakiyar yankin Hiran.
An ruwaito cewa mayakan sun cinna wuta a manyan motocin dakon kaya guda 2 makare da abinci da kuma wasu motocin bus dauke da fasinjoji a kusa da garin Mahas.
Tuni dai dangin wadanda suka gamu da ajalinsu suka fara tantace ’yan uwansu tare da rakiyar hukumomin Somaliya da kuma dakarun wanzar da zaman lafiyar na kungiyar tarayyar Afirka.
Wannan harin dai na zuwa ne wata guda bayan da kungiyar ta al-Shabaab ta kai hari tare da yin garkuwa da wasu mutane a wani shahararren otel da ke babban birnin kasar Mogadishu.
DW ya ruwaito cewa, akalla mutane 21 ne suka rasa rayukansu a wancan lokacin da aka kwashe tsawon sa’o’i 30 ana musayar wuta.
Wani jami’in tsaron kasar na cewa kungiyar ta al-Shabaab ta kara zafafa kai hare-hare kan fararen hula a cikin kwanaki biyun da suka gabata a yankunan Hiran da Galgaduud.