Kungiyar IS ta fitar da wani faifan bidiyo na wani mutum da ta ce shugabanta, Abu Bakr al-Baghdadi ne, wanda ya kuduri niyyar daukar fansa kan kasashen da suka fatattaki mayakansa daga yankunan da ta kwace a da a Syriya da Iraki.
Tun shekarar 2014 ba a sake jin duriyarsa ba, lokacin da ya bayyana a birnin Mosul cewa ya kirkiro wata kasar Musulunci a yankunan kasashen Syria da Iraki.
A sabon bidiyon, al-Bagdadi ya tabo batun fatattakar mayakansa da aka yi a Baghuz, wanda shi ne yanki na karshe da aka kwace daga kungiyar ta IS.
Babu tabacin lokacin da aka nadi bidiyon, amma IS ta ce a watan Afrilu ta nade shi.
An kuma wallafa bidiyon ne a shafukan Intanet na kungiyar mai suna al-Furkan.
Wani Kakakin Ma’aikatar Tsaro ta Amurka ya ce za su gudanar da bincike kan faifan bidiyon domin tabatar da sahihancinsa.
Bagdadi ya ce hare-haren bukukuwan Ista da aka kai a Sri Lanka, an kai su ne a matsayin wata ramuwar gayya saboda kwace garin Bakhuz na kasar Iraki, kamar yadda BBC ya ruwaito.
Ya ce wadansu mayaka daga kasashe kamar Burkina Faso da Mali sun yi masa mubayi’a, sannan ya ce zanga-zangar da ake yi a Sudan da Aljeriya alama ce ta nasara gare shi, saboda “jihadi ne kawai mafita,” inji shi.
Amurka ta ce a shirye take ta ci gaba da farautar shugabannin kungiyar ISIS da suka rage bayan bidiyo da aka fitar da ya nuna Abu Bakr al-Baghdadi.
Jami’an Amurka sun ce har yanzu suna nazari domin tabbtar da sahihancin bidiyon.
Gwamnatin Amurka ta ce yanzu ya nuna cewa yaki da ISIS bai kare ba, duk da kungiyar ta rasa yankunan da ta karbe a Syriya da Iraki.
A watan Maris ne dakarun Syriya na SDF da Amurka ke mara wa baya suka yi ikirarin murkushe daular ISIS bayan murkushe mayakanta a Syriya.