Hukumar Kula da Harsashen Yanayi ta Najeriya (NIMET) ta yi harsashen tafka ruwan sama mai yawa a wasu sassan kasar nan tsakanin ranakun Talata da Alhamis.
Hakan, a cewar hukumar na iya kawo tangarda a tashi da saukar jiragen sama a fadin kasar.
NIMET ta ce a cikin kwanaki uku masu zuwa, za a sami mamakon ruwan sama a Kudancin Jihar Kebbi da Yammacin Jihar Neja da Arewacin Katsina da Gabashin Kano da Jigawa da Bauchi da Yammacin Yobe da Gombe da Kaduna da Filato da Nasarawa da Kwara da kuma Abuja.
Harsashen dai na kunshe ne a cikin wani harsashe da NIMET fitar ranar Litinin.
Hukumar ta kuma ce akwai yuwuwar a sami tsaka-tsakin ruwan sama a Jihohin Kuros Riba da Akwa Ibom da Binuwai da Ebonyi da Sakkwato da Ekiti da Edo da Kogi da Ogun da Osun da Oyo da Enugu da Anambra da Imo da Abiya da Ondo da Legas da Delta da kuma Jihar Bayelsa a tsakanin ranakun.
A yankunan da ake sa ran samun ruwan da yawa, hukumar ta ce, “Akwai barazanar samun ambaliya a kan hanyoyi da gidaje da gonaki da gadoji wadanda za su iya kawo tsaiko ga tafiye-tafiye.
Sai dai NIMET ta shawarci jama’a kan su yi takatsan-tsan lokacin da za su fita ta hanyar kaurace wa wuraren da ke ajiye ruwa mai yawa da kuma wuraren da ruwa ke cin gudu.
Harsashen ya kuma kara da cewa, “Yawan ruwan a wadannan kwanakin zai disashe hasken gari, wanda hakan na iya jawo motoci su kauce daga kan hanya ko su yi hatsari ko ma a sami tsaiko a tashi da saukar jirage. Saboda haka, muna ba mutane shawara su kwana da sanin wannan yanayin don kaucewa samun matsala.”
Ko a ’yan kwanakin nan dai sai da wani ruwan sama ya shafe sassa da dama na Jihar Legas, inda motoci suka rika nitse wa, mutane da dama suka rasa muhallansu.