✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar rabin ’yan Afghanistan su fuskanci yunwa – MDD

Majalisar ta ce akwai yuwuwar matsalar ta ta’azzara yayin da sanyi ke tunkarowa.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa akwai yuwuwar fiye da rabin ’yan Afghanistan su fuskanci matsalar karancin abinci daga watan Nuwamba mai kamawa.

Hukumar Kula da Abinci ta Majalisar (FAO) da kuma shirin samar da abinci na majalisar (WFP) ne suka bayyana hakan a cikin wata sanarwa ranar Litinin.

A cewar sanarwar, illar matsalar karancin ruwan da aka fuskanta a kasar, da rikice-rikice da kalubalen annobar COVID-19 da kuma matsalar tattalin arziki sun matukar kawo cikas a harkar samar da abinci a kasar.

An kuma yi harsashen cewa akwai yuwuwar matsalar ta kara ta’azzara yayin da sanyi ke kara shigowa.

“Kowanne mutum daya daga cikin biyu a Afghanistan zai iya fuskantar yunwa a tsakanin watan Nuwamba da Maris mai zuwa.

“Wannan ne adadi mafi girma da aka taba samu cikin shekara 10 da majalisar ta gudanar da bincike kan matsalar karancin abinci a kasar,” inji sanarwar.

Shugaban WPF, David Beasley, ya ce lamarin na Afghanistan na cikin mafiya muni a fadin duniya, inda ya ce zai tilasta wa miliyoyin ’yan kasar ko dai su yi gudun hijira ko kuma su tsaya yunwar ta kassara su.

“Matukar ba mu yi wa tufkar hanci ba, yunwa za ta karu, kuma yara za su ci gaba da mutuwa, ba za mu ci gaba da yi musu alkawura da baki kawai ba,” inji sanarwar.

Ana dai harsashen cewa kananan yara ne matsalar za ta fi shafa, inda ko a ranar Lahadi sai da wani malamin addinin Musulunci ya sanar da cewa wasu yara su takwas ’yan gida daya suka mutu a yammacin birnin Kabul. (NAN