✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar ’yan ta’adda za su kai hare-hare Amurka —Birtaniya

’Yan ta’addan za su kai hare-haren a wuraren da aka fi samun baki.

Birtaniya ta fitar da wata sanarwa da ke gargadin cewa akwai yiwuwar ’yan ta’adda za su kai jerin hare-hare a Amurka.

Wannan dai na zuwa ne bayan kasashen biyu sun yi wa Najeriya makamancin wannan gargadi makonni kadan da suka gabata.

Cikin wata sanarwa da Ofishin Jakadancin Birtaniya da ke Amurka ya fitar ranar Juma’a, ya ce akwai yiwuwar ’yan ta’addan za su kai hare-haren a wuraren da aka fi samun baki da suka ziryarci Amurkan da kuma tashoshin sufuri.

“Maharan mutane ne masu ra’ayin ta’addanci, kuma za su kai harin ne a wuraren da aka fi samun cincirindon wadanda ba ’yan asalin Amurka ba,” a cewar sanarwar.

Gwamnatin Birtaniyar ta ce tuni Amurkar ta dauki azama inda za ta jibge jami’an tsaro a wuraren da jama’a ke taruwa, domin dakile hare-haren.

Haka kuma ta ce sashin tsaron cikin gida na Amurkan ya fitar da sanarwa kan fargabar aukuwar harin.