Wata kwakkwarar majiyar tsaro ta shaida wa Aminiya a Kotun da za ta yanke hukunci kan zaben gwamnan Kano cewa har yanzu ba su san inda alkalan kotun suke ba, kuma da alamar ba za zo zaman da kansu ba.
Majiyar ta ce akwai yiwuwar alkalan za su halarci zaman ne ta bidiyo ta intanet, su kuma yanke hukunci, bisa umarnin da suka samu daga sama, saboda wasu dalilai na tsaro.
- An hana ’yan jarida shiga kotun da za a yanke hukuncin zaben Gwamnan Kano
- ’Yan sanda sun far wa wakilan Aminiya da BBC a kotun zaben gwamnan Kano
Hakan na zuwa ne a yayin da ake yi ta tayar da jijiyar wuya a harabar kotun, bayan jami’an tsaro sun shaida wa bangarorin da ke shari’ar cewa mutum 50 kacal, ciki har da su da ‘yan jarida da lauyoyi kadai aka amince su shiga cikin kotun.
Aminiya ta kawo rahoton yadda aka tsaurara matakan tsaro a harabar kotun da kewaye domin tabbatar da doka da oda.