✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Raul ya maye gurbin Zidane a Real Madrid

Tuni Zidane ya yanke hukunci game da makomarsa.

Rahotanni daga kasar Spain na nuni da cewa kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya yanke hukuncin barin kungiyar a karshen kakar wasannin bana.

Rahotannin sun ce Zidane ya fara yin bankwana da ’yan wasansa, tun kafin wasan Real Madrid da Sevilla da aka yi kunnen doki a satin da ya gabata.

Ana kuma hasashen cewa Raul Gonzalez ne zai gaji kujerar Zidane.

Raul Gonzalez, wanda tsohon dan wasan gaban Real Madrid ne, yanzu yana horar da kungiyar kafan matasan Real Madrid ta Castilla.

Duk da cewar wasu kungiyoyi a kasar Jamus na zawarcin, amma ya nuna sha’awarsa na ci gaba da zama a Madrid.

Tuni masu sharhin kwallon kafa ke ganin da zarar Zidane ya ajiye aikinsa, Real Madrid za ta ba wa Raul dama don gwada irin tasa bajintar.