Rahotanni daga kasar Spain na nuni da cewa kocin kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Zinedine Zidane ya yanke hukuncin barin kungiyar a karshen kakar wasannin bana.
Rahotannin sun ce Zidane ya fara yin bankwana da ’yan wasansa, tun kafin wasan Real Madrid da Sevilla da aka yi kunnen doki a satin da ya gabata.
- Rashin tsaro: ‘Sai an yi wa Buhari addu’a’
- Masallacin Kudus: Isra’ila ta kai wa masallata sabon hari
- Abaya: Yadda gasar kayan Sallah ke sanya mata a hadari
- Ba kowane irin fim nake shiga ba — Tijjani Faraga
Ana kuma hasashen cewa Raul Gonzalez ne zai gaji kujerar Zidane.
Raul Gonzalez, wanda tsohon dan wasan gaban Real Madrid ne, yanzu yana horar da kungiyar kafan matasan Real Madrid ta Castilla.
Duk da cewar wasu kungiyoyi a kasar Jamus na zawarcin, amma ya nuna sha’awarsa na ci gaba da zama a Madrid.
Tuni masu sharhin kwallon kafa ke ganin da zarar Zidane ya ajiye aikinsa, Real Madrid za ta ba wa Raul dama don gwada irin tasa bajintar.