Kungiyoyin kwadago na NLC da TUC na alamta cewa za su iya dage zanga-zangar da suka shirya gudanarwa a fadin Najeriya a ranar Laraba.
Kungiyoyin dai sun shirya zanga-zangar ce don nuna rashin goyon bayansu ga abin da suka kira da “tsauraran manufofin tattalin arziki” na Shugaban Kasa, Bola Ahmed Tinubu.
- Ba gudu ba ja da baya kan zanga-zanga ranar Laraba — NLC
- Ba za mu lamunci tashin hankali yayin zanga-zanga ba -Sufeton ‘Yan sanda
Sakataren kungiyar na kasa, Emma Ugbaja, ne ya bayyana hakan ga manema labaran Fadar Shugaban Kasa, bayan an dage tattaunawar da suka tsara yi da gwamnatin Tarayya a dakin taro na Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.
Sai dai ya ce duk da matakan da Shugaba Tinubu ya sanar suna da kyau matuka, amma ba su wadatar ba.
Ya kuma ce za su tattauna da mambobins, wadanda su ne suke wakilta kafin su yanke shawarar mataki na gaba da za su dauka kafin dare ya yi.
A wani labarin kuma, Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban Kasa, Femi Gbajabiamila, ya bayyana kungiyoyin kwadagon a matsayin masu sauraro kuma yana da kwarin gwiwar za a sami maslaha kafin safiyar Larabar.