✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Akwai yiwuwar kai wa jiragen yakin da Buhari ya sayo harin ta’addanci —Majalisa

Jiragen yakin Super Tucano da Gwamnatin Buhari ta sayo suna fuskantar barazanar harin ’yan bindiga a Jihar Neja

Majalisar Tarayya ta ce jiragen yaki samfurin Super Tucano da Shugaba Buhari ya sayo da sauran kayan yakin gwamnati na fuskantar barazanar hari daga ’yan bindiga a Jihar Neja.

Wakilin mazabar Agwara/Borgu, a Majalisar Wakilai, Jafaru Muhammad, ya bayyana cewa hare-haren da ’yan bindiga suka yawaita a yankin da ke cikin mazabarsa, babbar barazana ce ga kayan yakin da aka girke a Sansanin Sojin Sama na 407 da ke garin New Bussa.

“Jiragen yaki samfurin Super Tucano da aka girke a Makarantar Koyon Sarrafa Makaman Yaki a Sararin Samaniya ta 407 da ke New Bussa na fuskantar barazanar hari da lalatawa, duba da kusancin wurin da maboyar ’yan bindiga da ke Gandun Daji na Kaiji da ke yankin Borgu.

“Sannan ana tsare da wasu gawurtattun ’yan kungiyar Boko Haram a barikin sojoji na Bataliya ta 221 da ta 101, wadanda  su ma tsararrun babbar barazana ce ga rayuka da dukiyoyin al’ummar da ke yankin mazabar,” inji dan majalisar.

Da yake gabatar da kudurin a ranar Talata, dan Majalisar ya bukaci Gwamnatin Tarayya da dauki matakan dakile hare-haren a yankin mazabar tasa da ke da kusanci da sansanonin sojin.

Ya bayyana wa zauren Majalisar cewa, tun da akwai wadatattun sojoji a sansanonin sojin da ke Wawa da New Bussa, to wajibi Gwamnatin Tarayya ta tura su domin su kare rauyu da dukiyoyi.

Jafaru Muhammed, a duk mako ’yan bindiga suna kai kazaman hare-hare gami da kona gidaje da lalata dukiyoyi a gundumomin Babanna da Malale da Wawa da Shagunu da Pissa/Kabe a Karamar Hukumar Borgu da kuma garin Mago da ke Karamar Hukumar Agwara.

Ya bayyana cewa munin lamarin ya kai ga kashe Hakimin Dekare da masu gadi da dama a Gandun Daji na Kaiji, aka kuma yi garkuwa da Hakimin Wawa da mahaifiyar wani dan Majalisar Dokokin Jihar Neja.

A cewarsa, tun da akwai wadatattun sojoji a sansanonin sojin da ke Wawa da New Bussa, to wajibin Gwamnatin Tarayya ta tura su domin su kare rauyu da dukiyoyi.

Tuni dai Majalisar ta amince da bukatar sannan ta umarci kwamitinta kan Ayyukan Agaji da Jinkai da Tasro ya tabbatar Gwamnatin Tarayya ta aiwatar da abin da zaman ya cim-ma matsaya a kai.