✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai yiwuwar Boris Johnson ya zama Fira Ministan Birtaniya a karo na biyu

Johnson na iya samun kuri'a 140 na goyon bayan komawarsa kujerar a karo na biyu

Akwai yiwuwar tsohon Fira Ministan Birtaniya, Boris Johnson ya sake komawa kan kujerarsa da ya yi murabus, bayan wadda ta gaje shi, Liz Truss, ita ma ta yi murabus.

Boris Johnson na cikin wadanda suke kan gaba cikin ministocin jam’iyyar Conservative da ake iya samu shugabancin jama’iyyar, domin zama Fira Minista.

“Akwai yiwuwar Boris Johnson ya dawo kan kujerar, ko da yake ba na so in bayar da tabbaci sosai, amma tabbar akwai abin mamaki a tattare da lamarin siyasar a yanzu,” in ji Tim Montgomerie, wanda ya assasa shafin intanet na ConservativeHome.

Tim Montgemerie ya ce Johnson na iya samun kuri’a 140 na goyon bayan komawarsa kujerar a karo na biyu – adadin da ya zarce 100 da kwamitin jam’iyyar ta kayyade.

“Boris Johnson ya fi farin jini a wurin talakawa a kan daya dan takarar na kan gaba, wato Rishi Sunak,” in ji Montgomerie a shirin Today na kafar BBC Radio 4.

Hakan na zuwa ne washegarin murabus din Fira Minista Liz Truss, mako shida bayan Mista Johnson ya yi murabus daga matsayin fira minista, bayan rikicin cikin gida ta sa ministocin jam’iyyarsa sun juya masa baya.

A halin yanzu magoya bayansa tsohon fira ministan na ta kiraye-kirayen ya shiga zawarcin kujerar ta shugaban Majalisar Ministoci.

Wasu kafofi da ba na hukuma ba a kasar na cewa Boris Johnson wanda ke hutu a kasar Jamhuriyar Dominican, ya samu goyon bayan akalla ministoci 50, wasu kuma na cewa 38 ne.

Jacoba Rees-Mog, shi ne minista na farko da ya bayyana goyon bayansa a bainar jama’a ga Boris Johnson, a ranar Juma’a, washegarin murabus din Liz Truss.

Tsohon Sakataren Kasuwanci kuma dan a-mutun tsohon fira ministan, ya wallafa a shafinsa na Twitter cewa, “Ina tare da Boris” sannan ya sa maudu’in #BORISorBUST.

A tsarin mulkin Birtaniya, Shugaban Jam’iyya mai mulki shi ne ke zama Fira Minista kuma Shugaban Majalisar Ministocin kasar.