Hukumar Kula da ’Yan Gudun Hijira da Wadanda Yaki ya Daidaita ta Kasa (NCFRMI) ta ce akwai ’yan gudun hijirar Najeriya kimanin 500,000 a kasashen waje da ke jiran a kwaso su zuwa gida.
Kasashen da mutanen suke dai inji hukumar sun hada da Nijar da Kamaru da Cadi da Mali da Libya da sauran makwabtan kasashe.
- Najeriya A Yau: Shin Najeriya kasa ce mai cikakken ’yanci?
- NDLEA ta kama mai kai wa ’yan bindiga kwayoyi da albarusai
Kazalika, hukumar ta ce akwai sama da mutum 73,000 da suka fito daga kasashe 23, wadanda ta yi wa rijista a matsayin ’yan gudun hijira a Najeriya.
Kwamishiniyar hukumar, Iman Suleiman Ibrahim ce ta bayyana hakan a asibitin sojoji na 44 da ke Kaduna, yayin rabon tallafin kekunan guragu da sauran kayayyaki ga asibitin.
An dai bayar da tallafin ne tare da gudunmawar Kungiyar Matan Sojoji da ’Yan Sanda (DEPOWA), a matsayin shirin hukumar na ‘yaki da yunwa’.
A cewarta, yawan tashe-tashen hankulan da Najeriya ke fuskanta ya kara yawan mutanen da suka rasa muhallansu zuwa sama da mutum miliyan uku, cikin shekara daya kacal.
“Mun bullo da wannan shirin ne don mu tallafa da kayan abinci da ma wadanda ba na abinci ba, ga wadanda ke da tsananin bukata, ciki har da jami’an tsaron da suka ji raunuka a bakin daga,” inji Iman.
Ita kuwa shugabar kungiyar ta DEPOWA, Misis Vickie Irabor, ta ce tallafin nuna yabawa ne ga sojojin da suka sadaukar da rayuwarsu wajen hidimta wa kasa.
Ta ce raunukan da mazajen nasu suka ji, ’yar manuniya ce ga sadaukarwarsu ga samun zaman lafiyar kasa, wanda a sakamakon haka mutane ke iya yin bacci da ido biyu.