Aminiya ta tattauna da sarkin maginan kasar Zazzau, wato sarautar Babban Gwani a gidansa da ke Unguwar Babban Gwani, a cikin Birnin Zariya, Jihar Kaduna, wanda shi ne na takwas daga cikin jerin wadanda suka tabe rike sarautar Babban Gwani a kasar ta Zazzau, inda ya yi bayanin irin rawar da gidansu ya taka wajen gine-ginen manyan gidajen masarautun gargajiya tare da wuraren ibada, masu kunshe da tarihi. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Aminiya: Ka gabatar da kanka ga masu karatu, da yadda aka yi ku ka samu sarautar Babban Gwani, wato sarautar sarkin maginan Zazzau?
Babban Gwani: Da sunan Allah mai rahama mai jin kai. Suna na Muhammadu Gidado Haruna Babban Gwani, wato sarkin magina kasar Zazzau, kuma ni ne sarkin magina na takwas a cikin jerin wanda suka riki sarautan Babban gwani. Ssarautar na da tarihi ne mai tsawo, sai dai mu yi bayanin abin da ya samu. Ita wannan sarauta ta Babban Gwani wato sarautar sarkin maginan kasar Zazzau, sana’ar gidanmu ta sa aka yi mana ita, kuma Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimu shi ne wanda ya nada mutum na farko da ya fara sarautan a wannan gida na mu mai suna Muhammadu Aliyu, kuma ana masa lakabi da Duguru. Kamar yadda tarihi ya nuna, asalinsu mutanen kasar Indunishiya ne, kaka Muhammadu mai Dugura mai suna Abdullahi tare da daansa Aliyu suka fito sana’arsu na gini, tare da kuma neman ilimi. A kan hanyarsu sai suka sami labarin cewa a Najeriya akwai ilimi, don haka suka kamo hanya zuwa Najeriya, to a kan hanyarsu ta zuwa sai Allah Ya yi wa Malam Abdullahi rasuwa. Don haka sai shi Aliyu ne Allah Ya sa ya ketaro Najeriya, kuma ta kasar Katsina ya shigo. To a wancan lokaci ya zauna a Katsina yana sana’arsa ta gini, kuma yana neman ilimi, to sai Allah Ya sa ya auri mata a Katsina, to shi ne ta Haifa mas da da aka sa ma suna Muhammadu, to bayan ya taso aka sashi makarantar allo kuma ana koya masa sana’ar gidansu ta gini, kuma ance sun yi karatu, da wasa tare da Ummarun Dallaje wanda ya yi sarki a Katsina, ana cikin haka sai shi Muhammadu ya sami labarin cewa Zariya akwai ilimi kowane iri, don haka sai ya bar mahaifinsa a Katsina ya nufo garin Zariya neman ilimi. To da Allah Ya kawo shi garin Zariya sai ya ci gaba da neman ilimi amma bai nuna kasa a sana’a na gini ba, tunda shi bako ne. Sai ya ci gaba da neman ilimi. Ana haka sai ya sami labarin cewa mahaifinsa ba lafiya, to sai ya tafi domin ya dubo shi, ashe Allah Ya yi wa mahaifin rasuwa. To kamar yadda aka ce, a wannan zamani Shehu Usmanu ya baiyana, to a baya na sanar da kai cewa sun taso tare da Ummarun Dallaje domin sun yi karatun Allo tare, to sai suka dunguma zuwa karbo tuta wajen Shehu Usmanu, bayan sun isa wajen Shehu sai aka ba Ummarun Dallaje tuta na sarauta aka ce shi Muhammadu ya rako shi domin ya mara masa baya wajen yin sarautan sai shi ya ce a’a shi yana da sana’a kuma yana bukata ya yi karatu, don haka ba zai yi sarauta ba. Sai Shehu ya tambaye shi cewa to wani irin sana’a yake yi? Ya ce sana’ar gini, sai Shehu ya ce to ai ko muna bukatar ka domin gina makarantu da masallatai, wanda hakan ya sa ya yi zamansa a can.
Aminiya: Ya aka yi shi Malam Muhammadu Babban gwani ya sake dawowa Zariya da zama har Allah Ya sa ya yi sarauta?
Babban Gwani: Madallah, a lokacin da Sarkin Zazzau Malam Abdulkarimu ya je mubaya’a na shekara shekara da sarakuna ke zuwa wajen Shehu sai ya ga irin ginin da shi Muhammadu Duguru ke yi ya ba shi sha’awa, sai ya roki Shehu da aba shi aronsa domin ya zo ya gina masa fadarsa wanda ze rika zaman sarauta, to bayan ya biyoshi, kuma ya yi mishi abin da yake so ya kammala sun sallame shi ya kuma, da shekara ya dawo sai Sarki Malam Abdulkarim ya kara komawa mubaya’a sai ya yi godiya da aikin da akayi mishi, sai kuma ya kara neman alfarma cewa a sake ba shi shi domin ya zo ya gina masa masallaci, to shi ne ya sake dawowa aka gina wancan Babban masallacin juma’a da kake gani na kofar fada. To a dalilin gina wannan masallaci ne Sarki Malam Abdulkarimu ya nada shi sarautar Babban Gwani wanda shi ne Allah Ya sa har zuwa yanzu sarautar ke gidanmu.
Aminiya: Baya ga Muhammadu Aliyu Duguru na farko a sarautan Babban Gwani sai wa?
Na biyu shi ne Sarki Mikailu Babban Gwani, sai na uku Ibrahim Babban Gwani, na hudu Jibrin Babban Gwani, sai na biyar Haruna Babban Gwani, sai Jafaru Babban Gwani, sai Haruna Babban Gwani, sai Jafaru Babban Gwani, sai kuma ni Muhammadu Gidado Babban Gwani a jerin sunayen wadanda suka rike sarautar gidanmu.
Aminiya: Ka ce kusan duk gidajen sarautar kasar nan kuna da sa hannu wajen ginasu, to kamar yaya ke nan?
Ka ga dai baya ga Katsina gida ne, kuma nan ne mafari, sai Sakkwato garin Shehu, kusan duk tsofafin masallatan da suke daular Shehu asalinsu gidan Babba Gwani ne, sai Masallacin Juma’a wanda Babban Gwani ya gina wa Sarkin Bauchi Yakubu, kuma ga masarautan Kano wanda a kan haka shi Sarki Babba Gwani ke da Unguwa a garin Kura a kofar kudu mai suna Unguwar Gandu inda sarki na wancan zamanin ya bashi domin ya yi noma na kan hanyar zuwa garin Kano, wanda har yanzu muna da tsatso a garin Kura wanda dangimu ne a sanadiyyar gina masarautan Kano da Babban Gwani ya yi, haka ma a garin Birnin Gwari shi ya gina masallacin garin da gidan sarkin, kuma akwai wasu gine gine zamanin turawa a Unguwan Wusasa da ke Zariya, daga cikinsu akwai babban wannan cocin wanda su Sarki Babba Gwani suka ginashi wanda ba zan san tsawon shekarun da cocin ya yi ba, kuma shi ne kusan na farko a Arewa kuma har yanzu idan ana bukatan ayi mishi wani gyara, gidan Babban Gwani ke aikin. Har zuwa yanzu kuma shi wannan cocin yana daya daga cikin tsofafin gine gine da Gwamnatin Taraya ke kula da su yanzu. Haka kuma masallacin juma’a na kofar fadan sarkin Zazzau yau yana da shekara kusan 181, domin a shekara na alif dubu daya da dari takwas da talatin da shida aka ginashi. Kasan da irin wadannan ginin ana yi wa sarakuna ne da masu sukuni wato attajirai na da, kuma kasan da a cikin daki ake yin adon, ba a fili ba kamar yanzu domin da sai a cikin dakuna, to ka ga ai ba kowa za ka shiga da shi dakin ka ba, kai kadai kake kallon adon da aka yi maka, daga baya aka dawo ana yinsa a kofar gida ko a zauruka.
Aminiya: To har yanzu ana neman ku akan harkan irin wannan aiki naku?
kwarai kuwa masu sarauta da masu arziki duk suna sha’awar gini irin namu har gobe.
Aminiya: To kai wane irin rawa ka taka wanda zamu gani a yau?
To mu ai a yanzu sukuwa ta kare, sai dai zamiya. Amma har yanzu ruwa na maganin dauda. Muna cikin masu gyare gyari a yanzu, ka ga dai ni na yi aikin gyaran da aka yi ma kofar doka da dai sauran abin da ba za a rasa ba.
Aminiya: Batun iyalifa?
Ina da mata biyu, yara musu rai guda goma sha tara.