Fitacciyar jarumar fina-finan Hausa, Hauwa Waraka, ta ce mutane da dama na yi wa ’yan fim kallon ’yan Wuta, inda ta ce da suna da mukullin Wuta ko na Aljanna, da Wuta za su kai galibin ’yan fim.
Sai dai jarumar ta ce hakan sam ba ya bata mata rai saboda ta san babu mai Wuta da Aljanna sai Allah.
- LABARAN AMINIYA: Zargin Batanci: Abduljabbar Ya Nemi A Sauya Masa Kotu
- Shugaban Amurka ya kamu da COVID-19 duk da an yi masa rigakafinta
Hauwa Waraka ta bayyana hakan ne a wata hirarta da Sashen Hausa na BBC a cikin shirinsu mai suna ‘Daga Bakin Mai Ita’.
A cewarta, “Ni abin da nake fada wa al’umma, na san mutum dai ba shi da mukullin Wuta, ba shi da na Aljanna bare ya ce ai ni ne mai makullin Wuta, Wutar zan kai ki, ko kuwa ni ne mai makullin Aljanna, Aljanna zan kai ki.
“Don akasarin mutane kallon da suke yi mana da su suke ba da Wuta da Aljanna da ba za su ba dan fim Aljanna ba. Magana ta gaskiya saboda kallon da suke mana.
“Saboda akwai mutanen da za ka ji ko sunana aka kira sai ka ji sun ce wannan makamashin wutar? To ni kuma na ga ba ka da Wuta ba ka da Aljanna. Allah ne yake ba da ita, ba mutum ba.
“Ni kuma na san wacece ni, na san tsakanina da Ubangiji, kuma na san zuciyata, shi ya sa ni duk abin da mutum zai fada, wallahi ba ya damu na,” inji Hauwa Waraka.
Da aka tambayeta dalilin da ya take fitowa a matsayin wacce ba mutuniyar kirki ba a fim, jarumar ta ce a zahiri ba haka take ba, suna yi ne don su fadakar da masu yin halin don su daina.
“Ni ga duk lokacin da aka sa min kyamara ba na jin nauyin komai. Amma na san dai kamar busa sigari ko gidan karuwai, irin abubuwan da suke yi na san a addininmu da al’adarmu ba kyau, amma kuma muna yi ne don mu fadakar da masu yi kan illar abin cewa ba abu ne mai kyau ba.
“Shi ya sa idan za a nuna irin wadannan matan, dole sai an nuna iurin abin da suke yi. Dalilin da ya sa ake ba mu irin wannan muna yi, amma ba wai da gaske ba ne. Ni a zahiri babu abin da nake sha,” inji ta.