✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai masu daure wa ’yan Boko Haram gindi a Arewa –Rabaran Maina

Rabaran Joshua Ray Maina shi ne sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi a kwanakin baya ne ya karbi ragamar shugabancin kungiyar…

Rabaran Joshua Ray Maina shi ne sabon shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa (CAN) reshen Jihar Bauchi a kwanakin baya ne ya karbi ragamar shugabancin kungiyar daga Rabaram Lawi Pita Pokti wanda ya shugabanci kungiyar na tsawon shekara uku, a tattaunawarsa da wakilinmu, Rabaran Maina ya yi fashin baki game da rikita-riktar tsaro da siyasar Najeriya kamar haka:

Me za ka ce game da abubuwan da ke faruwa a jihohin Arewa?
Gaskiya mutanen Arewa maso Gabas muna cikin wani mawuyacin hali sakamakon matsalolin tsaro da muke ci gaba da fuskanta, kullum sai ka ji an kashe mutane kuma idan ka duba sosai za ka fahimci cewa babu shiyyar da take fama da talauci da jahilci kamar Arewa maso Gabas.
A Arewa maso Gabas muna fama da koma baya a fannonin tattalin arzikin kasa, mata da dama sun rasa mazajensu sakamakon abubuwan da ke faruwa a jihohin Borno da Yobe da Adamawa da wasu manyan biranen Arewa  irin su Kano da Kaduna da makamantansu.
Mun gagara gane ina ne tushen ’ya’yan kungiyar Boko Haram, akwai masu amfani da sunan addini suna cutar bayin Allah wajen gasa musu aya a hannu, wajibi ne al’umma ta fadaka kan halin da muke ciki.
kungiyar CAN reshen Jihar Bauchi tana da alaka mai kyau tsakaninta da sauran kungiyoyin addinai saboda haka za mu ci gaba da gudanar da ayyukanmu tare domin ciyar da jihar gaba.
Babu dalilin da zai sa Musulmi da Kirista su rika fada a tsakaninsu, kasuwa daya muke zuwa, saboda haka ina fatar za mu ci gaba da zama lafiya da junanmu.
Me za ka ce game da ’yan siyasar da za su yi amfani da malaman addinai a zaben 2015?
Babban abin da za mu fara yi shi ne wayar da kan al’umma, amma ya kamata a san cewa talakawa ma suna ba da gagarumar gudunmawa wajen lalata siyasar Najeriya. Abin da ya sa na fadi haka shi ne kullum sun fi son dan siyasar da zai ba su kudi maimakon wanda zai yi musu ayyukan raya kasa.
Malaman addinai da ake ba su makudan kudi a lokacin yakin neman zabe su ji tsoron Allah. Kowa ya ci ladan kuturu sai ya yi masa aski. Kuma duk dan siyasar da ya ba ka kudi a lokacin zabe haramun ne ka karbi kudin saboda kowa ya san cewa kudin jini ne. Ya kamata mu zabi mutanen kirki masu gaskiya da rikon amana wadanda a shirye suke su magance matsalolin al’umma, su ya kamata mu zaba a shekarar 2015.
Men ene sakonka ga ’yan siyasar da suke neman mulki ido rufe?
Babban sakona ga ’yan siyasar da suke neman mulki ido rufe shi ne su ji tsoron Allah su fahimci cewa Allah Shi ke ba da mulki ga wanda Ya so ba sai mutum ya yi tsafi ba, kowane dan Adam Allah Ya tsara masa abubuwan da zai samu a duniya.
’Yan a fasa kowa ya rasa ku tausaya wa al’umma kowa ya ga sakamakon rashin zaman lafiya a Arewacin Najeriya. Harkokin kasuwanci sun tsaya cik, mata an kasha mazajensu, kananan yara an kashe iyayensu sakamakon wadannan tashe-tashen hankula.
Tsohon Shugaban kasa Cif Olusegun Obasanjo ya yi mulki na tsawon shekara takwas daga bisani ya nemi tazarce amma bai yi nasara ba. Haka shi ma Shugaba Jonathan koda za a kara masa shekaru hudu ba zai kammala ayyukan da ya sa a gabansa ba.
Saboda haka a shekara ta 2015 dole Shugaba Jonathan ya tafi wani ya zo ya ba da tasa gudunmawa wajen bunkasa rayuwar al’umma. Idan kuma Allah Ya ce sai Shugaba Jonathan ya sake mulki a 2015, babu wani dan Adam a duniya da ya isa ya taka masa birki, wannan shi ne abin da na yi imani da shi a matsayina na Kirista.
Abin da muke fata shi ne mu samu zaman lafiya da bunkasar tattalin arziki a shekara ta 2015.  Kashe-kashe sun yi yawa a Najeriya kullum sai ka ji an kashe dimbin mutane a jihohin Najeriya.
Saboda haka kullum ina fada cewa babu dattawa a wannan shiyya na Arewa sai tsofaffi, me ya sa wadannan bama-bamai suka yi yawa a Arewa ba mu da dattawan da za su fito fili ne su fadi gaskiya ko suna tsoron mutuwa ne?
Don haka ’yan siyasa muke da su a Arewa amma ba dattawa ba, ya kamata duk wani dan Arewa ya fahimci haka.
A karshe mene ne sakonka ga ’yan Arewa?
Babban sakona shi ne ina kira da babbar murya ga Shugaba Jonathan ya san cewa zai amsa tambayoyi Ranar Gobe, game da yadda ya tafiyar da Najeriya. Idan mutum daya ya rasa ransa sai ya ba da amsa a gaban Allah.
Bayan haka masu zagin Shugaba Jonathan da mukarrabansu su ma su ji tsoron haduwarsu da Allah, shugabanci yana da wahala amma sai mai hankali da zurfin tunani ne ya san haka.
Na yi imani da Allah za a iya magance rikicin Boko Haram cikin kankanen lokaci, amma akwai wadanda ya kamata su yi magana a Arewa sun rufe bakinsu. Akwai masu daure wa ’yan kungiyar Boko Haram gindi don haka suke cin karansu babu babbaka.