Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i, ya yi zargin cewa akwai makiyan dan takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar APC, Bola Tinubu a Fadar Shugaban da suke kokarin ganin sun kai shi kasa.
Ya bayyana haka ne yayin tattaunawarsa da gidan talabijin na Channels, a cikin shirinsu na Sunrise Daily da safiyar Laraba.
- Hisbah ta wanke matar da ta auri saurayin ’yarta a Kano daga zargi
- Har yanzu farin jinin Buhari na nan a Kano – Fadar Shugaban Kasa
El-Rufa’i ya ce mutanen, wadanda bai bayyana sunansu ba, sun fusata ne tun lokacin da aka kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani na APC.
Ya kuma ce mutanen na fakewa da bukatar ganin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi abin da ya dace.
Ya ce, “Na tabbatar a cikin Fadar Shugaban Kasa akwai masu son mu fadi zaben nan, saboda bukatarsu ba ta biya ba, an kayar da dan takararsu a zaben fid-da gwani.
“Wadannan mutanen na kokarin fakewa da bukatar Buhari ya yi abin da ya dace. Zan bayar da misalai biyu; wannan batun na biyan tallafin mai wanda ya ke sa Najeriya ta kashe makudan kudade abu ne da dukkanmu mun dade da amincewa a cire shi.
“Sai da ma na tattauna da Shugaban Kasa a kan haka, inda na nuna masa dalilin da zai sa dole a cire. Saboda ta yaya zaka ware biliyan 200 don manyan ayyuka sannan ka kashe tiriliyan biyu wajen biyan tallafi? Wannan maganar muka tattauna da shi a 2021, kuma aka amince za a cire saboda kudin sun tashi sosai.
“Misali na biyu kuma shi ne canjin kudi. Ya kamata a fahimci Shugaban Kasa. Mutane na zargin Gwamnan CBN, amma ba haka batun yake ba. Idan muka koma tarihi, ko zamanin mulkin Buhari na soja, ya canza kudi saboda maganin barayi da masu jibge haramtattun kudade a gida.
“Manufa ce mai kyau, kuma Shugaban Kasa yana da dalilansa na yin hakan, amma yin hakan cikin kankanin lokaci kuma ana tunkarar zabe bai da wani amfani,” in ji Gwamnan.
Kalaman na El-Rufa’i dai na zuwa ne mako daya bayan Tinubu ya yi zargij akwai masu yi masa zagon kasa a cikin jam’iyyarsa, wadanda ya ce ba sa so ya lashe zaben.
Dan takarar ya yi zargin cewa da gangana aka kirkiro wahalar man fetur da canja fasalin kudi domin a yi masa zagon kasa.