✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai maganin ciwon ido na jabu a kasuwannin Najeriya – NAFDAC

NAFDAC ta ce magungunan na da matuƙar illa ga idanu

Hukumar da ke Kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Kasa (NAFDAC), ta gargadi ’yan Najeriya kan ci gaba da amfani da wasu magungunan ciwon ido da yanzu haka suke yawo a kasuwannin Najeriya.

Hukumar ta ce magungunan ne na EzriCare da kuma Delsam, kuma tuni aka bayar da umarnin janye su daga kasuwanni.

Umarnin daina amfani da magungunan na kunshe ne a wata sanarwa ga jama’a mai lamba 008/2023, mai dauke da sa hannun Shugabar hukumar, Farfesa Mojisola Adeyeye, a Abuja ranar Lahadi.

Ta ce an janye magungunan ne a watan Fabrairu bayan an sami rahotannin gurbatarsu da wani sinadari mai cutarwa ga lafiyar idanu.

Ta ce tun bayan sanarwar, Hukumar Dakile Yaɗuwar Cututtuka ta Amurka (CDC) ta bayar da rahoton yadda marasa lafiya 68 suka kamu da cuta, a Jihohi 16 na kasar.

A cewar Farfesa Mojisola, “Sauran matsalolin da aka gano maganin na haddasawa sun hada da dauke gani gaba daya da cire kwayar idanu da kuma mutuwa sanadiyyar taruwar jini.”

Ta ce binciken da aka yi a dakunan gwaje-gwaje sun nuna akwai kwayoyin cuta a cikin maganin nau’in EzriCare bayan yin gwaje-gwaje mai yawa.

Shugabar ta NAFDAC ta ce yanzu suna ci gaba da bincike domin gano ko an sami matsala ne a ainihin wajen sarrafa maganin.