Hukumar Zabe ta Kasa (INEC), ta ce akwai Katunan Zabe kusan dubu 300 wadanda ba a karba jibge a ofishinsu a Jihar Imo.
Hukumar ta ce wannan abin damuwa matuka, ganin yadda jama’ar yankin ke nuna rashin damuwa da zuwa karba katin zabensu.
- Saudiyya ta soke gwajin COVID-19 da yawan shekaru a Hajjin 2023
- Jarirai 200 aka haifa a sansanin ’yan gudun hijirar Binuwai —SEMA
Kwamishinan INEC na Jihar, Farfesa Sylvia Agu ce ta bayyana haka a Owerri, babban birnin jihar yayin taron masu ruwa da tsaki ranar da aka gudanar ranar Laraba.
A cewarta, “Imo na da Katunan Zabe kusan 300,000 wadanda ba a karba ba jibge a ofisoshinsu da ke kananan hukumomi 27 na jihar.”
Kamfanin Dillancin Labarai Na Najeriya (NAN), ya rawaito cewa, katunan na wadanda aka yi wa rajista ne a baya.
Agu ta ce, hukumar ta karbi katunan zabe guda 152,221 na sabbin wadanda aka yi wa rajista a jihar, kuma ta fara rabarwa.
(NAN)