✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai illoli a tattare da buga sunayen masu taurin bashi – Mikati

Alhaji Shuaibu Idris Mikati tsohon ma’aikacin banki ne, wanda a yanzu masani ne mai ba da shawara mai zaman kansa kan tattalin arziki. A wannan…

Alhaji Shuaibu Idris Mikati tsohon ma’aikacin banki ne, wanda a yanzu masani ne mai ba da shawara mai zaman kansa kan tattalin arziki. A wannan tattaunawar da Aminiya, ya bayyana hanyoyin da ya kamata a dawo da tattalin arzikin kasar nan kan turba.

Aminiya: Me ye ra’ayinka game da buga sunayen masu taurin bashi a jaridu?
Mikati: Ni dai a ra’ayina hakan bai dace ba domin an yi ne kawai don a kunyata wasu. Wannan ba zai sa a biya bashin ba. Domin wasu daga cikin masu taurin bashin suna da dalilai kwarara na kasa biyan.
Aminiya: Shin watanni ukun da aka bayar na a biya basussukan sun wadatar?
Mikati: Watanni ukun da aka diba ba su wadatar ba don wadanda sukaci babban bashi su biya. Misali shine idan wanda ya ci bashi kuma ya na son ya biya, amma ya sa gidan sa a kasuwa har watanni uku suka wuce ba a sayar ba to ya ya za ayi.
Aminiya: Shin wannan zai daga darajar tattalin arzikin kasar nan?
Mikati: Bana tsammanin wannan zai yi wa kasar nan alfanu. Sai dai zai yi wa harkar banki illa matuka, domin jama’a za su guji karbar bashin banki, wanda shi ne babban dalilin da ya sa ake kafa bankuna.
Aminiya: Ko wannan zai daga darajar kudin Najeriya wato naira?
Mikati: Wannan ba zai daga darajar naira ba. Domin abubuwan da ke daga darajar kudin kasar nan kamar naira bai da cudanya da karfafa darajar aikin banki.
Aminiya: Kana ganin wannan zai kawo masu zuba jari daga kasashen waje zuwa Najeriya?
Mikati: Hakan ba zai sa masu zuba jari daga kasashen ketare su yi gogoriyon zuwa kasar nan ba. Sai dai ya sa su guji kasar don in sun karbi bashin suka kasa biya a kan lokaci za a yi musu tonon silili.
Aminiya: Me ya sa ’yan Najeriya ke da taurin bashi, ko ba sa son wasu su karu ne?
Mikati: Ba a Najeriya ne kadai ake da taurin biyan bashi ba. A kasahen Amurka da China da Japan da kuma Birtaniya ana samun taurin bashin kamfanoni. Bai dace ba a ce a nan ne kadai ake da taurin bashi ba. Akwai dalilai da yawa da ke janyo bashi ya wuce lokacin biyansa.
Aminiya: Me ya sa ma’aikatan bankuna ke karya dokokin aikin banki?
Mikati: Da wuya ace lallai ga dalilin da ya sa manyan ma’aikatan banki ke yi wa dokan cin bashin banki karan-tsaye. Amma bai rasa nasaba da rashin kwararrun ma’aikatan banki, da masu tunawa masu bashi cewa su fara biyan bashi tun kafin lokaci ya kure, da kuma zargin wasu ma’aikatan bankin da yin kuruciyar bera, wannan ya shafi halayyar matune daban-daban.
Aminiya: Me ya sa ake saurin yankewa masu kananan laifi hukunci amma ake jan-kafa wajen ma’aikatan banki?
Mikati: Ina zargin sai an yi harkan shari’ar kasar nan garanbawul dungurungum. Domin ana dadewa ba a kammala shari’ar manyan mutane da ma’aikata ba. Domin dadewa ba a kammala shari’ar ba nakasu ne. Ya dace alkalai su jajirce don aikin su. Sannan a gyara kotuna don yin aikin cikin sauki.
Aminiya: Me ye shawararka ga wannan sabuwar gwamnatin Muhammadu Buhari?
Mikati: Ya dace gwamnatin ta bude ido sosai domin, sauraren mashawarta na kwarai da kuma samar da yanayin da kayan aiki na kwarai, dakile cin hanci da rashawa, samar da ilimi da tsaro. Sannan kuma a inganta aikin gona da hako ma’adinai don samar da kudin shiga bai kawai daga man fetur ba.