✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Akwai hannun ‘na gida’ a harin kurkukun Kuje – Ahmed Lawan

Ya ce akwai hannun ma'aikaci ko wanda ya taba aiki a gidan

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmed Lawan, ya ce babu yadda za a yi harin da aka kai kurkukun Kuje da ke Abuja ya yi nasara in babu sa hannun wasu wadanda ya kira ’yan cikin gida.

Ya kuma vce harin ’yar manuniya ce kan irin kalubalen da ke cike da harklar tsaro a Najeriya.

Ya bayyana hakan ne lokacin da ya jagoranci wata tawagar Sanatoci zuwa ziyara gidan yarin ranar Alhamis domin ganin irin barnar da maharan suka yi a ciki.

Mutanen da ke cikin tawagar sun hada mambobin Kwamitin Leken Asiri na Majalisar, kuma shugaban Hukumar Kula da Gidajen Gyaran Hali ta Najeriya (NCoS), Halliru Nababa, ne ya zagaya da su.

Ahmed Lawan ya kuma zargi hukumar da gaza samar da kyamarorin tsaro na CCTV a gidan da ma sauran gidajen yarin kasar nan.

Daga nan sai ya roki shugaban na NCoS da ya aike da bukatar samar da kyamarorin tsaron domin a shigar da su kasafin kudin 2023 da za a gabatar wa Majalisar Dokoki ta Kasa.

Ya ce, “Mun sami labarin sama da mutum 300 ne suka zo a kafa yayin harin. Ya kamata a ce an ga alamun tahowar tasu kafin su karaso.

“A tashin farko ma babu yadda za a yi mutum 300 su zo su kaddamar da irin wannan harin ba tare da yin shiri ba. Dole sun shafe kamar mako daya ko ma wata daya. Ya kamata a ce jami’an tsaronmu sun gano haka kafi lokacin.

“Sannan yadda suka rika shiga daki-daki suna sakin masu laifi, musamman wadanda aka tabbatar ’yan ta’adda ne, akwai alamomin tambaya masu yawa a ciki.

“Dole aikin dan cikin gida ne, wani wanda ya taba aiki a nan, ko kuma yanzu yake aiki a ciki,” inji shi.