Hukumar Tsaron Farin Kaya (DSS) ta sanar cewa ’yan Majalisar Dokoki ta Tarayya suna fuskantar barazanar kisa ko garkuwa da su domin karbar kudaden fansa.
DSS ta bayyana hakan ne a daidai lokacin da ’yan majalisar da sauran ’yan Najeriya ke shirye-shiryen tafiya hutu domin bukukuwan karashen shekara, a yayin da matsalar tsaro ta ki ci, ta ki cinyewa.
- Kisan Sakkwato: Masarautar Bichi ta shirya addu’o’i na musamman ranar Juma’a
- Monguno ya bayyana sunayen kungiyoyin da ke daukar nauyin ta’addanci a Najeriya
“Wadannan mutane suna cikin hadarin kisa, sacewa, garkuwa da su, yi musu fashi, ko suddabarun siyasa,” inji sanarwar da kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya fitar.
Karon farko ke nan da hukumar ta ambaci ’yan Majalisar Tarayya kai-tsaye a jerin mutanen da ke cikin hadarin garkuwa da su ko yi mu kisan gilla a Najeriya.
A baya hukumar kan yi wa ’yan majalisar kudin goro ne a cikin manyan mutane idan ta tashi fitar da gargadin jerin mutanen da ke cikin hadari ko barazanar tsaro.
A baya-bayan nan dai an ji wasu daga cikin ’yan Majalisar suna kokawa cewa lamarin matsalar tsaro a yankunan da suke wakilta ta kai makura, ta yadda su da kansu ba sa iya zuwa garuruwansu.
‘Ku kasance cikin shiri’
Da take karin haske a kan sanarwar, hukumar ta bukaci ’yan majalisar da ’yan siyasa da ma’aikatan gwamanti da sauran jama’a da cewa su kasance masu lura da yanayin tsaro, “domin kar ku fada cikin hadarin hari da miyagun makirce-makirce.”
A cewar Afunanya, hukumar ta gano shirin bata-gari na amfani da dalibai da za su tafi hutu su shigar da su ayyukan ’yan bindiga da garkuwa da mutane da fashi da tayar da tarzoma da shan miyagun kwayoyi da sauran miyagun laifuka.
Afunanya ya ce bata-garin sun riga sun wuce gona da iri, saboda haka ya shawarci “duk masu daukar nauyin wadannan miyagun ayyuka a yankin Arewa ko Kudu, cewa su sake tunani su daina, idan kuma ba haka ba hukumar za ta shafa wa idanunta toka ta murkushe su.”
Sanarwar ta DSS ta kuma gargadi shugabannin addini na da siyasa da na al’umma da su yi hattara da furucinsu a yayin da lokacin zaben 2023 ke kara matsowa, domin hukumar ba za ta bar wani mahaluki ya tayar da zaune tsaye a Najeriya ba.
“Hukumar na kira ga duk masu yin hakan da su daina, sannan tana kira ga ’yan siyasa su bi ka’idojin da aka shimfida su guji furta kalamai ko aikata duk wani abu da zai iya tayar da fitina ko wargaza kan jama’ar Najeriya a gabanin zaben 2023.”